Labarai

Ƴan ƙato-da-gora sun kama ɗan Boko Haram 1, sun hallaka 3 a hanyar Maiduguri-Damaturu

Gamaiyar jami’an tsaro na sa kai, CJTF, waɗanda a ka fi sani da ƴan-ƙato-da-gora da su ke taimakawa sojoji yaƙi da ƴan ta’adda a Arewa-maso-Gabas sun damƙe wani ɗan ta’adda guda ɗaya sannan su ka hallaka guda uku yayin da su ke satar amfanin gona a kan hanyar Maiduguri-Damaturu.

Jaridar PRNigeria ya rawaito cewa ƴan-ƙato-da-gora ɗin sun kwantar da ƴan ta’addan bayan da su ka kaiwa wasu manoma hari sannan su ka dace musu amfanin gona.
Wata majiya ta shaidawa PRNigeria cewa a ranar Alhamis ne da misalin ƙarfe 3:30 na yamma ƴan ta’addan su ka kaiwa manoman hari a kusa da ƙauyen Daiwa.majiyarmu ta samu wannan labari daga daily Nigerian hausa
Majiyar ta ce “sai ƴan ta’addan su ka harbi manoman inda su ka kashe mutane biyu su ka raunata guda ɗaya.

“Ai kuwa sai dakarun bijilant ɗin, a ƙarƙashin jagorancin kwamandan sashin binciken sirri na CJTF ɗin, Saminu Audu su ka datse ƴan Boko Haram ɗin a Lamboa, tsakanin Minok-Janaka a kan hanyar Maiduguri-Damaturu.
“Bayan wani ƙazamin faɗa, sun samu nasarar hallaka uku da ga ƴan ta’addan inda a ka cafke guda da ransa.

“Ƴan ta’addan ire-iren sauran yaran Abubakar Shekau ne da su ka ƙi yin mubaya’a ga ISWAP. Su sun dogara ne da garkuwa da mutane da kuma fashi domin su sami abin da za su ci,”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button