Zan Tsaya Takarar Dan Majalisar Tarayya Na Bakori Da Danja -Rarara
Rarara ya tabbatarwa da leadership hausa haka a Katsina a wata zantawar da ya yi da shi, akan wasu batutuwa da suka shafi wakokinsa musamman wakar da ya ce talakawa ne suka biya kudin yin ta da kuma batun tsayawarsa takara.
Ya kara da cewa ya zuwa yanzu akwai batun sabuwar wakar da ya yi wanda talakawa suka biya kudi domin bayyana ayyukan shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya ce kwanan nan zai tsunduma bin jahohin Najeroya domin nuna irin ayyukan da ya gano Buhari ya yi.
“Idan Allah yasa na kammala wannan aikin da ke gaba na, to zan tsaya takarar dan majalisar tarayya na kananan hukumomin Bakori da kuma danja, idan kuma wannan aiki ya sha gaba na, sai kuma a duba batun nan gaba.” Inji shi.
A cewarsa ya yi niyyar gano ayyukan shugaban kasa guda 90 amma sai ya gano dubu 900 wanda yake ganin aikin yana da yawa, amma dai idan ya samu damar kammala wannan aikin zai dawo akan batun yin takararsa wanda tuni ya fara yawo a gidajen soyasa.
Rarara wanda ya bayyana cewa zaban shugawabannin siyasa da aka gudanar a satin da ya gabata a Ktsina abin ya yi masa kyau, kuma ya yi yadda ake so, saboda haka yana fatan cewa wannan zaban zai taimaka wajan kara samun nasarar jam’iyyarsu ta APC a zabe mai zuwa.
Ya kuma yaba da irin tsarin da aka bi wajan samar da shuwagabannin wanda ya ce abin ya yi matukar burgeshi, kuma a Najeriya babu inda aka yi abinda ya da ce kamar jihar Katsina, wanda ya ce hatta shugaban kasa ya yaba da kokarin gwamna Masari akan haka
“idan ka duba da kyau, tun daga zaban shuwagabanni na matakin runfuna da kananan hukumomi da na jiha babu wanda ya ce bai yarda da tsarin da aka bi ba, saboda haka wannan shi ne ake kira shugabanci, Masari ya yi matukar kokari wajan hada kan ‘yan jam’iyyar APC a jihar Katsina “ inji Rarara
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina