Yadda Fasto ya jagoranci Kiristoci suka je taya Musulmai murnar Maulidi a jihar Kaduna
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Fasto Buru ya bayyana cewa ya kai ziyara filin wasan ne domin ya taya murnar zagayowar ranar haihuwar Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Jaridar Labarunhausa ta ruwaito cewa wannan taron Maulidi da aka yi tsakanin addinan biyu an yi shi ne domin kara dankon zumunci tsakanin al’umma da kuma zaman tare.
Fasto Buru ya ce:
“Annabi na kowa ne ba tare da la’akari da yare, al’ada, launin fata, kasa ko nahiya ba, saboda ya yi wa’azi domin a zauna lafiya har zuwa karshen rayuwar shi.”
Ya bayyana cewa a matsayin shi jakadan zaman lafiya kuma shugaban Kiristoci, zuwan shi wajen Musulmai bai canja masa addini daga Kiristanci zuwa Musulunci ba.
Faston ya kara da cewa:
“A lokacin Kirsimeti Musulmai daga yankuna da yawa na Arewacin Najeriya sun saba zuwa su gudanar da taron Kirsimeti da Kiristoci, a kokarin da suke na ganin sun samar da kyakkyawar alaka tsakanin m.”
Ya roki duka mabiya addinan biyu da su yi amfani da wannan lokaci su fadakar dangane da kaunar juna, hadin kai, da kuma zaman lafiya a Najeriya baki daya.
Fasto Buru ya kuma yi kira ga dukkanin Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci na Maulidi wajen yin addu’a kan Allah ya kawo karshen wannan tashin hankali da ake fama da shi a Najeriya.
Ya ce:
“Tilas mu dinga tunawa da cewa duka mun fito daga tsatso daya ne wato, Annabi Adam da Hauwa’u. Mu ‘yan uwa ne da kowanne ya yadda da littafin shi na Qur’an da Bible, kuma duka mun yadda da mutuwa da kuma ranar tsayuwa, saboda dole mu kula da junan mu.”
Mutane na ta tofa albarkacin bakinsu bayan wani babban Fasto yayi bikin Sallah a Masallaci tare da Musulmai
Babban Fasto, Peter Ayanbadejo ya sanya mutane suna ta tofa albarkacin bakin su a shafukan sadarwa bayan an nuno shi a cikin babban Masallacin jihar Ogun, tsakiyar Musulmai yana bikin babbar Sallah.
Hotunan babban Malamin Kiristan tare da al’ummar Musulmi na ta yawo a shafin sadarwa na Facebook.
Reverend Father Ayanbadejo shine babban Malamin cocin Katolika Deanery dake Ogbere.
A wasu daga cikin hotunan an nuno Faston yana zaune akan tabarma a tsakiyar Masallacin. Haka kuma an nuno shi yana daukar hoto tare da Musulmai dake cikin Masallacin.