Kannywood

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya
Akwai wasu jarumai a masana’antar shirya fina-finan Hausa Kannywood da suka taba neman gwada sa’arsu a fagen siyasar Najeriya
A wannan rubutun mun tattaro muku fitattun jarumai 5 da suka taba neman wata kujerar siyasa a yankunan su
Daga cikinsu har da furodusan fim ɗinnan mai farin jini ‘Izzar So’ wato Lawan Ahmad daga jihar Katsina
Ƙano – A cikin masana’antar fina-finan Hausa wacce aka fi sani da Kannywood, akwai wasu jarumai da suka taba kokarin nuna bajintarsu a fagen siyasa.
Waɗannan jarumai sun fito takara a matakai daban-daban na yankunansu, kuma a dokar ƙasa kowa na da damar fitowa takara matukar ya cike ƙa’idojin hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC.
Ga sunayen jaruman da kuma mukaman siyasa da suka nema, kamar yadda Aminiya,legit sunka rahoto.
1. Hamisu Iyantama
Hamisu jarumi ne da aka jima ana fafatawa da shi a masana’antar Kannywood, kuma ya taba fitowa takarar gwamnan jihar Kano a shekarar 2007.
Jarumin ya fito takarar ne ƙarƙashin jam’iyyar ND, amma Malam Ibrahim Shekarau na ANPP ne ya ƙashe zaɓen a wannan lokaci.

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya
Hamisu iyantama

2. Alasan Kwalle
Alasan sananne ne a Kannywood musamman a shirye-shiryen barkwanci kuma yana ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a masana’antar.
 
Jarumin ya nemi takara da dama, cikinsu harda takarar shugaban ƙaramar hukumar Ungogo da ya nema a shekarar 2007 ƙarkashin PDP. A wannan lokaci ya kare a matsayin ɗan takarar mataimaki.
Hakanan kuma ya tsaya takarar kansila a gundumarsa Bachirawa dake Ungogo karkashin inuwar jam’iyyar APC a shekarar 2015.
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya
Alhassan kwalle

 
3. Nura Hussain
Nura na ɗaya daga cikin jaruman Kannywood da suka jima ana damawa da su, ya fito takarar Kansila a mazaɓar Yakasai, ƙaramar hukumar Birni da Kewaye, cikin jihar Kano, a shekarar 2007.
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya
Nura Hussaini

4. Abba El-Mustapha
El-Musatapha ko Abba Ruda kamar yadda aka fi saninsa, jarumi ne da ya yi tashe kuma ya jima a masana’antar shirya fina-finan Hausa.
 
Abba ya taba neman tikitin takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Gwale ta jihar Kano, karkashin jam’iyyar PDP a 2015.
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya
Abba ElMustapha

Sai dai Abba Ruda bai samu nasara ba, domin bai samu tikitin tsayawa takarar ba tun a wurin zaɓen fidda gwani.
5. Lawan Ahmad
Wannan jarumi ya jima tauraruwarsa na hasakawa a Kannywood, a halin yanzun shine furodusan fim mai dogon zango ‘Izzar So.’
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya da mukaman da suka nema Hoto: @lawanahmad
Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa a Najeriya
Lawal Ahmed

Lawan Ahmad ya taba neman tikitin takarar ɗan majalisar jihar Katsina mai wakiltar mazaɓar Bakori ƙarakashin jam’iyyar APC amma bai samu tikitin ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button