Addini

Jan Hankali Mai Muhimmanci Kan Hukuncin Auren Mutu’a – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Jan Hankali Mai Muhimmanci Kan Hukuncin Auren Mutu'a - Sheikh Aminu Ibrahim DaurawaNikahul mut’ati’ wato auren mut’a. ,shi ne mutum ya auri mace izuwa wani ƙayyadajjen lokaci.
Wannan auren duk da za’a iya samun cikar wasu sharuɗan a cikinsa , misali ana samun soyayya,da amincewar mace. Kuma aka samu yardar waliyi da sadaqi, da shaidu.
Sai dai an sanyawa auren lokacin karewarsa duk ƙarancinsa da yawan sa shine dalilin ɓacinsa.
Sanya wannan lokacin shi ne abin da ya ɓata auren, tunda shi aure ana yinsa ne da niyyar zama sai mutu ka raba , ko kuma su ma’auratan su rabu bisa zaɓin kansu saboda da wani dalili. Banda wannan ma , babu wanda yake da tabbacin kaiwa lokacin da za’a sanyawa auren tsakanin ma’auratan. Misalin yadda ake auren shi ne waliyi zai ce ya ɗaura aure tsakanin wane da a wance , akan sadaki kaza izuwa lokaci kaza. Akan samu shedu, amma waɗancan sharuɗa guda huɗu su ne mafiya muhimmanci wato mai aure da wacce za’a aura da sadaki da siga da kuma iyaka lokacin da za’a yi zaman aure. Da zarar wannan lokaci ya cika to aure ya kare , koda kuwa awa ɗaya ne ko yini guda.
Sanyawa aure lokaci ƙarewa ko yin aure da niyyar saki na daga cikin auren da malamai suka ce ba su halatta ba.
Auren mut’a halal ne a farkon musulunci kamar yadda abubuwa da yawa suke halal, kamar shan giya da makamantansu. Amma daga baya manzon Allah (SAW), Allah ya soke ya kuma haramta shi har izuwa ranar Alƙiyama. Da farko an fara soke shi ne , sokewa ta wucin gadi. Idan lalurar halatta shi ta zo sai a bayar da dama , kamar idan an samu kai a halin tafiya ko wata matsananciyar buƙata ko wata sha’awa mai karfi wacce za a iya tunkuɗa mutum zuwa yin zina.
. Daga baya kuma bayan cikar addini da kammaluwarsa aka soke shi har abada. Da wannan zaka haɗa tsakanin hadisan dake nuni da cewa an soke auren mut’a a lokuta mabambanta.
Kamar yadda malamai ma’abota ilmi da bibiyar dalilai suka tabbatar. Don haka dai , a ƙarshe an soke auren mut’a a fathu Makka kuma babu wani dalili da ya zo da yake ɗauke wannan haramcin.
Akan wannan dukkan mazahabibin musulunci suke tafi , Malikiya da Shafi’iya da Hambaliya da Hanafiya da ragowarar malamai da ake izina da maganarsu.
SHEKARAR DA AKA HARAMTA AUREN MUT’A
Saɓanin da malamai kawai suka yi shi ne a wace shekara aka haramta auren mut’a , amma basu yi saɓani akan haramcinsa ba.
Wasu malaman suka ce an haramta shi ne a shekara ta bakwai da hijra a yaƙin Khaibara kamar yadda ya tabbata daga Sayyidina Ali, ya ce da Abdullahi ɗan Abbas : Manzon Allah (SAW) ya hana auren mut’a, ya hana cin naman jaki a lokacin khaibara.
Buhari 5115, da Muslim 1407..
Wasu kuma suka ce an haramta shi ne a shekara ta 8 bayan hijira, wato lokacin da aka yi fatahu Makka. Kamar yadda ya zo a hadisin ibn Samra, babansa ya ce sun yi yaƙi tare da Annabi (SAW) lokacin fatahu Makka, ya ce muka zauna a Makka kwanaki goma sha biyar.
Manzon Allah (SAW) ya bamu izni, ya bamu dama mu auri mata amma da niyyar in za mu koma za mu rabu da su. Saboda haka muka yi irin wannan auren. Ya ce ba mu fita daga garin Makka ba; har sai da Manzon Allah (SAW) ya ce mana wannan auren daga yau an hana shi. Muslim 1406.
A wata riwayar cewa ya yi Matan da muka aura sun kasance tare da mu da niyar za mu sake su zuwa wani lokaci, kwana uku. Sai manzon Allah (SAW) ya yi umarni da a rabu da su, ma’na kada a sake yin irin wannan aure. Kamar yadda ya zo a hadisin muslim 1406.
. A wani lafazin yake cewa Manzon Allah (SAW) ya umarce mu da yin aure zuwa wani lokaci a lokacin da aka yi fatahu Makka. Kuma ba mu fita daga Makkan ba har sai da aka soke wannan auren.Muslim 1406.
Wasu malaman suka ce an haramta auren mut’a ne shekarar da aka yi yaƙin “Au’ɗas” kamar yadda ya tabbata a hadisin Salamatu bn Ak’ wa’i yake cewa Manzon Allah (SAW) ya yi mana sauƙi a yaƙun Au’ɗas da yin mut’ar kwana uku . Wato mu auri mata da niyyar bayan kwana uku ko wata uku za mu sake su, sannan kuma sai aka haramta shi.
Amma dai kamar yadda muka gabatar an haramta auren mut’a daga ƙarshe. Sannan duk hadisan dake nuni akan haramcinsa a wata shekara , suna nuni da cewa ne kawai wannan haramcin na wucin gadi ne. Kafin daga bisani a haramta shi har abada. Kamar yadda aka dinga haramta shan giya lokaci bayan lokaci a matakai dabam dabam .
JAN HANKALI MAI MUHIMMANCI AKAN AUREN MUT’A
A nan wurin yana da kyau mu ja hankalin mutane dangane da wasu fatawowi da hadisai da za su iya ji ko su yi karo dasu dake nuni da cewa an samu wasu daga sahabbai dake ganin halaccin auren mut’a har bayan wafatin ma’aiki. Kamar yadda ya zo a hadisin Jabir bn Abdullahi, wanda yake cewa : ” mun kasance mukan auri mata da nufin zuwa wani lokaci za mu sake su, kuma mukan basu ma abin da bai wuce tafin hannu na dabino ko tafin hannu na gari ba. Wannan a lokacin Manzon Allah (SAW) da lokacin Sayyidina Abubakar duk muna yin haka. Har sai lokacin da Sayyidina Umar ya hau gwamnati sannan ne ya hana mu
Anani malamai suna bayar da amsa ne da cewa , wannan ya faru ne saboda ɗayan abubuwa biyu :
1- Kodai hadisan da suka haramta auren mut’a bai je ga waɗannan sahabbai ba ne har sai da sayyadina Umar ya tabbatar musu da shi , sai suka hanu. Kamar yadda dama sau tari akan sami wani sahabi yana bayar da wata fatawa kafin wani hadisi ya zo masa. Idanya ji hadisin sai ya sauka daga fatawarsa ta farko.
2- Ko kuma hadisin ya zo masa amma bai fahimce shi , a haramcin na din din din ba. Ya fahimce shi ne a haramci na wucin gadi , wanda wata lalura zata iya sawa a yi sassauci , kamar yadda hakan ya faru tun Manzon Allah ya raye.
Akan Wannan zamu fahimci fatawar Abdullahi ɗan Abbas dake ganin halaccin auren mut’a idan akwai lalura. Har yake cewa auren mut’a kamar cin naman mushe ne saboda tsoron halaka. Kafin daga bisani ya janye , daga wannan fatawar , ya tabbatar da haramcinsa har abada.
Waɗannan abubuwa kuwa a fili suke , musamman idan aka yi la’akari da ƙarancin kafaɗen sadarwa a wanzan zamani. Wanda ko a wannan zamani akan sami mutane da yawa basu sami wani labari ba , tare da cewa an yaɗa shi a kafafen sadarwa , ko kuma su sami labarin amma su yi masa wata fahimta ta dabam har sai an nusar da su yadda abin yake. Wannan kuwa ya sha faruwa har a zamanin Manzon Allah , a sami wani sahabi ya fahimci wata aya ko hadisi fahimta ta dabam , har sai daga bisani an nusar da shi fahimta ta dai dai. Misalai akan waɗannan suna da yawa.
A taƙaice dai , hadisin Jabir da fatawar ɗan Abbas ba dalilai ne na halaccin auren mut’a ba, kamar yadda malamai suka tabbatar , kamar kuma yadda su kansu sun sauka daga wannan fatawar ba akanta suke ba.
Banda wannan Allah ne kaɗai ya san irin fitina da ɓarna da taɓarɓarewar al’amura da za’a samu idan aka buɗe ƙofar auren mut’a. Kuma yana daga abin takaici a yanzu a riƙa samun ɗalibai a manyan makarantu su na yin auren mut’a ba tare da sanin iyayensu ko wakilansu da alummar gari ba.
Kuma wani abin mamaki shi ne , masu ganin ya halatta a yi auren mut’a suna ƙyamar a yi da ƴaƴansu ko ƙannensu ko ƴan uwansu. Suna kuma ƙyamar a dangata auren ga malamansu ko jagororinsu da limamansu. Sannan duk wanda ya kalli yadda ake auren mut’a a zamanin jahiliyya zai ga cewa ya sha bambam da irin auren mut’ar da ake kira a yi na wannan zamani. Manufar wancan shi ne kamewa daga zina. Manufar wannan kuwa ita ce holewa da morewa , tunda zaka samu mutum yana da mata babu wata lalura a tare da shi , amma yana da matan mut’a barkatai.
Ƙari akan haka , auren mut’a irin wanda wasu ke kira izuwa gare shi , aure ne da zai ruguza kyakkyawan tsari na zamantakewa da cakuɗewar nasaba da yawaitar ƴaƴa marasa tartibin uba da saɓani da rikici irin wanda ake ji kuma ake gani cikin al’ummar da ta yarda da shi.
Allah ya tsare mana addininmu da mutuncin mu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button