Labarai

Gyatuma Yar Shekara 82 Tayi Wuff Da Dan Shekara 36 (Hotuna)

Wata mata yar kasar Ingila tayi wuff ko auren caraf da shantalelen saurayi wanda bayan aurensa ta nuna dole sai an bashi biya ya dawo da zama Burtaniya inda amaryarsa yar kasar ce.
Kamar yadda shafin Daily Nigerian Hausa sun ruwaito kamar haka

Gyatuma mai shakaru 82 ta kafe sai an ba wa angonta dan shekara 36 biza

Wannan Baturiyar kasar Ingila mai suna Iris Jones, ta ce idan ba’a ba wa mijinta Mohamed Ibriham biza ba, sai rijiya.

Iya Iris dai ta hadu da wannan santalelen saurayi da ta yi jika da shi a manhajar Facebook, daga bisani ta niki gari har kasar Masar don haduwa da shi a watan Disambar 2020.

Bayan haduwar su, su ka yi aure, sai ta dawo Birtaniya. Tun bayan wannan lokaci ne dai ake ta tata-burza kan batun ba shi biza don tarewa da amaryarsa a kasar Birtaniya.

A watan gobe dai ake sa ran ofishin jakadancin kasar Birtaniya zai dauki mataki akan batun bizar Mohamed.”

Ga hotunan nan kasa ku kalla.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button