Labarai

Dalilin Da Yasa Nake so Iyaye Su Soke Kayan Lefe Da Kayan Daki – Fauziyya D Suleman

Dalilin Da Yasa Nake so Iyaye Su Soke Kayan Lefe Da Kayan Daki - Fauziyya D SulemanShahararriya marubucin nan fauziyya d suleman shugaban mai taimakawa gajiyayu ta creative helping needy foundation ta yi korafi akan a soki lefe da kayan daki inda ta kawo dalili da dama sosai wanda tabbas abun duniya ne ganin yadda iyaye mata basu iya yiwa yayansu kayan daki.

Inda bidiyon nata ya samu martani ko muce korafe korafe da ta wallafa shi ga mutum daya da munka kawo nasa sharhin.
Ga bidiyon nan ku kalla.

Sharhin wani Mutum Kowa Naka Yana mai cewa: Malama Fauziyya wallahi ku Iyaye Mata kune matsalar aure a yanzu,saboda kun fi karfin maza da yawa a cikin sha’anin auratayya a yanzu.Ma’ana sau tari za ki ga matsalar daga wajen Mata take bullowa.ya kamata kiyiwa Mata nasiha akan rawar da suke takawa a harkar auratayyar yaansu.

ki kallin misalin Shirin ku na Dadin Kowa a wajen auran Nuhu kansila,wannan ya ishi Mai hankali misali.kuma hanyar warware wannan matsalar ita ce,mu Kuma zuwa ga Allah kawai.Namiji ya fito Yana son yarinya,mafi yawa mahaifi bai Isa ya taka rawar a zo a gani ba,saboda yadda Iyaye Mata suka mayar da Aure da sha’aninsa.
Matukar ana son a Sami gyaran da kike son a samu,to,sai uwa ta yarda cewa uban yarinya shine yake da iko akan aurar da “yarsa dari bisa dari,a barshi ya taka rawarsa a matsayinsa na Mai gida.

Amma mafi yawan matayenmu na yanzu sun Raina mazajensu musamman a cikin al’umarmu ta Hausawa.Ni da ace zan baki wata shawara,da sai ki kirkiri want shiri na wayar da kan al’umarmu a game da wannan matsalar,mu Kuma ta hakane zamu shigo cikin Shirin dan dada wayar da kan al’umarmu.Allah yasa kin fahimci inda na dosa ameen.Ngd

Inda ita kuma fauziyya ta mayar masa da martani kamar haka.

Kowa Naka Kowanaka Idan kaga an raina namjii ka bincika da kyau shi ya fara raina kansa ta hanyar kasa sauke nauyin da ke kansa, namjin da ke kokari akan iyalinsa ba su isa yace su sauya ba.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button