Da sana’ar gwangwan na fara neman kuɗi – Tijjani
Tijjani ya kuma ce yayi sana’ar karen mota kafin ya kai ga shiga masana’antar Kannywood.
Jarumin ya bayyana hakan a zantawar sa da Freeom Radio.
Asase ya ce “Babban abin da yake burgeni a rayuwa shi ne na ga matashi ya riƙe sana’a komai ƙanƙantar ta, sannan mutum ya kasance mai gaskiya da rikon amana”.
Jarumin dai na fitowa a fina-finai Kannywood, kuma mafi yawa ana ganin sa yana taka rawa a matsayin ɗan fashi ko kuma wani gawurtaccen mai laifi.
“Babban abinda yake haifar da ƙwacen waya a yanzu shi ne rashin dogaro da kai da matasa ke yi, gashi kuma suna yiwa masu ƙananan sana’o’in kallon banza”. A cewar Asase.
Jarumi Asase yayi fatan masana’antar su ta ci gaba da samar da fina-finan da za su sauya rayuwar al’umma.