Labarai

[Bidiyo] Yadda za ku gane idan kuna da kansar nono

[Bidiyo] Yadda za ku gane idan kuna da kansar nono
Kansar mama ita ce cutar daji da mata suka fi fama da ita inda take shafar aƙalla mace miliyan biyu da dubu ɗari ɗaya duk shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.
An ware watan Okotoban kowace shekara a matsayin watan wayar da kai kan cutar sankarar mama a faɗin duniya.

WHO ta kuma ce cutar kansar mama ita ce cutar da ta fi janyo mace-macen da suka danganci cutar daji a mata.

Amma hukumar ta ce idan aka gano ta da wuri, ana iya warkewa daga cutar ta sankarar mama. Shi ya sa ma ake yawan bai wa mata shawarar yin gwaji akai akai.

Sai dai abin tashin hankalin shi ne idan ba a shawo kan cutar da wuri ba tana iya sanadin da za a yanke wa mace mamanta don samun sauƙi.

A wannan bidiyon, wata ƙwararriyar likita Hajiya Zainab Bagudu Shinkafi, ta yi mana bayanin yadda mata za su iya duba kansu don gane ko sun kamu da kansar nono.
Ga bidiyon nan ku saurara da bbchausa na zanta da ita.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button