Kannywood

Ban taba rubuta wakar Buhari ba- Cewar Rarara

Ban taba rubuta wakar Buhari ba - Cewar RararaA cewar Rarara: “Yawancin wakokin da nake yi wa Buhari suna zuwa ne daidai da lokaci, ba wai zama nake na rubuta waka akan shi ba.
“Misali ai na yi wakar Masu gudu su gudu na yi ta lokacin da Buhari ya ci mulki, a lokacin ana maganar idan PDP ta ci mulki sai dai mu gudu mu bar Najeriya.
“To Buhari ya ci mulki muma sai muka mayar da marta ni, a wakar, muka ce in kasan ka yi sata ka gudu.
Rarara ya ce a haka aka yi wakar ‘Ga Buhari ya dawo’lokacin Shugaban kasa ya yi rashin lafiya ya je Landan sai aka yi sa a ya ji sauki zai dawo, to a wannan lokacin cikin dare aka yi waƙar da aka ce washegari zai dawo, gaskiya ba na rubuta wakokin Buhari.”
Ga bidiyon domin ji daga bakinsa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button