Addini

Bai Kamata Malamin Addini Ya Shiga Cikin Ƙazantar Siyasar Najeriya Ba – Prof Ibrahim Maqarfi

Kuma Ina Tausayin Duk Malamin Da Ya Shiga Harkar Siyasa - Cewar Farfesa Ibrahim Maƙari

Bai Kamata Malamin Addini Ya Shiga Cikin Ƙazantar Siyasar Najeriya Ba - Prof Ibrahim Maqarfi
Bai Kamata Malamin Addini Ya Shiga Cikin Ƙazantar Siyasar Najeriya Ba – Prof Ibrahim Maqarfi

A cikin wata tattaunawa ta musamman da aka yi da Malamin a Ofishinsa, ya bayyana kuskure da rashin dacewar shigar Malaman Addinin Musulunci cikin gurɓatacciyar Siyasar da ake dagulawa a Najeriya.

Domin a cewar Malamin, kwata-kwata hujjar da wasu Malaman da ke shiga siyasa ko ake bawa muƙamai a tafiyar Gwamnati, su ke fakewa da shi na gyaran da za su kawo, ba karɓaɓɓe ba ne. Domin ba su ke da wuƙa da naman zartarwa ko canja abun da duk su ke kallo a matsayin kuskure ba, tun da umarni za a dinga ba su na abun da ake so, kuma dole in dai su na son kasancewa akan muƙaman na su, su yi yadda ake so ba yadda su ke so ba.

Wanda wannan zai sauƙe su daga turbar gayawa Shugabanni gaskiya zuwa yi musu biyayya akan ɓatar da su ke kai ɗin.
Akan haka ne Malamin ya ke ganin, zai fi kyau Malami ya tsaya daga waje ta dinga da’awa da kira ga mai aikata ɓarna don ya daina, maimakon shiga cikin ɓarna da ƙazantar ta sa, da zimmar tarayya da shi kamin ka tsamo shi daga wannan ƙazanta (Siyasa/Muƙamin).

Za ku iya kallon cikakken bidiyon yadda tattaunawar ta mu da Malamin ta kasance, kamar yadda nagudu tv na wallafa a shafinsu na tashar yourtube

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button