Addini

Auran Wuff Da Auran Caraf – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Advertisment

Auran Wuff Da Auran Caraf - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Wannan wata sabuwar Sara ce ta take yawo a social media, shine:
Idan wata mata mai yawan shekaru da abin hannu ta auri wani saurayi ko wani mai ƙarancin shekaru sai kaji ana cewa ta yi wuf da shi,
Idan kuwa namiji mai shekaru da yawa ya auri, karamar yarinya sai kaji ana cewa ya yi caraf da ita.
Hukuncin irin wannan aure yana da mahanga guda uku, a addinance, al’adance, a lafiyance,
Shin irin wannan aure ya saɓawa addini ko al’ada ko lafiya?
A addini babu laifi ayi aure tare da bambancin shekaru idan kowa daga ciki ya gamsu, mace tafi miji shekaru, ko shi ya fita shekaru babu wata matsala a addini, musamman idan an duba wata masalaha.
Ta ɓangaran al’ada ma babu matsala domin surutu ne ake yi saboda ba a fiye samun haka ba, musamman ta ɓangaran matan, saboda wasu suna ga kamar an yiwa saurayi wayo idan ya auri babba ko kuma ace Kwadayi ya kai shi,
Ta ɓangaran lafiya kuwa akwai jita jita na cewa idan mutum ya auri tsohuwa za ta kassara shi,
Haka cikin abin da yake jigo a rayuwar aure akwai karfin gamsar da juna yayin mu’amalar aure.
Duk sanda aka wayi gari ɗaya daga cikin ma’aurata ba zai iya biyawa ɗan uwansa buƙata ba , to akwai babbar matsala.
Daga cikin abin dake kawo gazawa wajen biyawa juna buƙata akwai bambamcin shekaru tsakanin ma’aurata ta yadda ake samun tazarar shekaru masu yawa tsakanin miji da mata.
Matsalar dake faruwa ita ce mutum ya kai hamsin ko fiye da haka sai ya je ya nemi auren ‘yar shekara 15 . Bambanci da ke tsakanin su yake shekara 35 Abin da zai faru ansan galibi shi ne a lokacin da ya kai shekata saba’in ƙarfinsa ya fara ƙarewa , ita kuma ta shekara talatin , wato dai dai cikar karfinta da buƙatuwarta izuwa na namiji.
Ita ƙarfinta ya kawo sha’awarta ta ƙaru shi kuma ƙarfinsa ya ƙare sha’awarsa ta yi baya.
Sai a wayi gari tana da buƙata amma ba zai iya biya mata ba. Kaga matsala ta faru kenan.
A irin wannan hali ne idan ba a samu mace mai tarbiyya da ilmi da tsoron Allah ba sai a wayi gari da aurenta tana neman maza. Ko direban gida ko yaron gida ko maƙoci kai an samu masu neman ƴan uwansu na jini.
Ba wani abu ya haifar da wannan ba sai kasantuwar mijinta ƙarfin shi ya ƙare ba zai iya gamsar da ita ba. Shi kuma ya ɗauko ta tana ƙarama gata akan ganiyar buƙata.
Wannan yana faruwa da yawa a ɓangaren maza. Sai dai abin bai taƙaitu akan maza ba kawai.
A ɓangaren mata su ma akan samu matar da shekarunta sun tura , amma ta auri matashi wanda yake kan ganiyarsa , wata ƙila ko dan tana da kuɗi ko wani dalili na kuruciyar zuciya.
Karshe sai a dinga samun matsala wajen kwanciyar aure. Idan ba a yi sa a ba , sai a wayi gari yana tare da ita saboda kuɗinta da matsayinta. Amma a gefe yana sharholiyarsa da ƴan mata. kuma wani sai ya je ya auro wacce ta gime shi a shekaru. Duk wannan abin da muke faɗa ba wai haramun ba ne a shari’a. Amma yana dai yana da kyau duk sanda za a yi aure a dinga duban maslahar auren da abin da zai je ya dawo. Ba bambancin shekaru kawai ba , hatta yanayin zamantakewar shi ma abin dubawa ne.
Za mu fahimci irin wannan darasin daga hadisin Jabir ɗan Abdullahi lokacin da ya auri bazawara tare da ƙarancin shekarunsa. Da manzon Allah ya ce masa ina ma budurwa ya aura. Sai ya yi uzuri da cewa ya auri bazawara ne mai hankali saboda mahaifinsa ya yi shahada ya bar masa ƴan mata guda tara. Idan ya auro wata budurwar sun zame masa goma kenan, sai gida ya zamo babu mai gudanar da shi. Irin wannan hangen nesan ya kamata a dinga aiki da shi duk lokacin da maganar aure ta taso.
Ya kamata mutane su riƙa lissafi na wacce irin mace ce zasu aura, su dinga la’akari da bambamcin dake tsakaninsu na shekaru , wadata . dangi , ƙabila , yare da sauransu , da irin tasirin da za su yi idan an yi auren.
Allah ya sa mu dace

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button