An maka jaruma Hafsat Idris gaban kotu kan cinye wasu makudan kudade da ta yi
Wani rahoto da gidan Radio Dala FM dake Kano ya kawo a jiya ya bayyana cewa wani kamfani ya kai kararr jarumar Kannywood Hafsat Idris, zuwa gaban babbar kotun jahar Kano, wacce ke Ungoggo, kan zargin cinye zunzurutun kudi har naira miliyan daya da dubu dari uku da aka bata domin daukar bidiyon rawa, amma ta saba alkawari.
Rahoton ya bayyana cewa jarumar ta zo gurin bikin, har an fara daukar bidiyon, sai kumaa ta gudu ba ta dawo ba, inda hakan yasa kamfanin ke bukatar kotu ta sa ta dawo musu da kudin su, kana ta biya su naira miliyan goma.
Sun bukaci wannan naira miliyan goma ne a matsayin diiyyar asarar da ta sa suka yi domin, sun tara ma’aikata sun dauko hayar kayan aiki, sai kuma rashin cika alkawarinta yasa sun yi asara.
Har ya zuwa yanzu dai bamuu ji ta bakin ita jaruma Hafsat Idris kan wannan batu ba.
Ku kasance da hausaloaded domin a duk lokacin da munka samu wani karin bayyani daga jarumar ko kuma kamfanin ko wani labarin da ya danganci wannan labari in sha Allah bazamuyi kasa a gwiwa ba zamu kawo muku shi da gaggawa.