Allah Ya Sa Hajiya Rabi Kwana Casa’in Ta Yi Wuff Da Ni – cewar Ibrahim Balarabe Wambai
Jaridar Manuniya ta hango wani wallafa da wani mazaunin lardin Zazzau, Ibrahim Balarabe Wambai ya yi inda ya nuna bukatuwarsa na son jaruma, Hajiya Rabi, wacce ta ke bayyana a wani shirin Hausa na “Kwana Casa’in” ta yi wuff da shi.
Mutunin, mazaunin wani gida da a ke ma lakabi da “Gidan Tuwo” a kasar Zazzau ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumuntan Facebook inda ya bukaci jama’a da su taya shi da Addu’a, don shi fa da gaske ya ke yi.
A zancensa ya ke cewa;”Don Allah ku taya ni da Addu’a, da gaske na ke yi – Allah ya sa Hajiya Rabi kwana Casa’in ta yi wuff da ni.”
Makaranta, ya ya ku ke ganin fatan Ibrahim Balarabe Wambai na jarumar ta yi wuff da shi?