Kannywood

Abinda Yasa Nake Tsinuwa Da Zage Zage A Fim – Musa Mai Sana’a

Abinda Yasa Nake Tsinuwa Da Zage Zage A Fim - Musa Mai Sana'a
Duk lokacin da aka ambaci jarumi Musa Maisana’a a cikin harkar fim, abin da mutane su ke fada, shine ya cika yawan tsinuwa a cikin fim din sa.
To sai dai a cikin tattaunawar du suka yi da wakilin Dimukaradiyya a game da tsinuwa ko zage zagen da ya ke yi jarumin ya kare kan sa in da ya ke cewa.
” Ka san su mutane ba sa tsayawa su kalli fim daga farko har karshan sa kafin su ya ke hukunci, kuma shi fim sai an kalla daga farko zuwa karshe a ke fitar da sakon da ya ke ciki.”
Ya Kara da cewar kuma shi zagi ko tsinuwa, al’ada ce ta Malam Bahaushe, don sai ka ga da wuya ka ji in mutane suna magana da wuya ba su yi zagi ko tsinuwa da la’anta ba.
To ni ina nuna wannan abin a matsayin ba daidai ba ne. Don haka idan na yi a cikin fim daga karshe za ka na zo na nuna ba daidai ba ne, saboda haka mutane su rinka kallon sakamakon da ya ke zuwa daga karshe ba Wai abin da jarumi ya ke yi daga farko ba”.
“Mutane su gane duk wani abu da mu ke yi a cikin fim, muna yi ne don fadakar da al’umma, don haka muna koyar da mutane yadda za su gudanar da rayuwar su ne cikin tsarin da kuma yadda za su rayu da ‘ya’ yan su, don su daina zagin su da tsine musu, saboda karshe zagin ya kan yi tasiri ga rayuwar yaran da suka haifa, don haka a rinka kula zagi ba shi ne tarbiyya ba, addu’a tagari a wajen iyaye ga yaran su ita ce za ta sa su tashi da tarbiyya. ”
Daga karshe Musa Maisana’a ya yi kira jama’a da mu rinka yi wa juna fatan alheri, domin shi ne zai kai mutane ga nasara, don haka idan an ga wani ya yi ba daidai ba, a yi masa addu’a ko a yi masa Nasiha ko koma a yi masa fata nagari.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button