Kannywood

Abin da ya sa muka rabu da miji na, inji mawakiya Ummi Kano

Abin da ya sa muka rabu da miji na, inji mawakiya Ummi Kano
Ummi kano

Fitacciyar Mawakiya a masana’antar finafinai ta Kannywood, wadda ta kware a wakokin siyasa Aisha Isah Usman Wadda aka fi sani da Ummi Kano Maidaraja, ta bayyana irin rabuwar da suka yi da mijin ta bayan sun samu arzikin yara biyu a tsakanin su da sunan abin al’ajabi ne da har yanzu tana tunanin sa.
Ummi Kano ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Dimukaradiyya dangane da yadda ta gudanar da rayuwar ta ta baya kafin ta shiga harkar waka. In da take cewa

“Duk da cewar na fara waka kafin na yi aure tun ina makarantar Islamiyya, da kuma na yi aure sai na daina yi sai daga baya da aure na ya mutu muka rabu da miji na sannan na dawo harkar waka.”

Dangane da rabuwar auren na ta kuwa cewa ta yi.
“Allah ne ya kawo rabuwar mu da mijina Amma ba Wai don ba na son sa ko ba ya so na ba, muna matukar son juna da mijina, sai dai saboda wani sabani na akida tsakanin gidan mu da mijin nawa ya sa aka raba auren mu. Kuma lokacin da aka raba auren namu yana kuka ina kuka a haka muka rabu da shi, sai dai har yanzu muna yi wa juna fatan alheri. ”
Daga karshe ta ce” A yanzu babban burina da na Mahaifiya ta shi ne na samu miji na yi aure, kuma ina fatan Allah ya cika mini burina da na Mahaifiyata.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button