Abin da ya faru da Maryam Booth na shirn faruwa da mawaƙiya Tiwa Savage
A lokacin da take tattaunawa da wata tashar rediyo a ƙasar Amurka, mawakiyar ta ce ba za ta biya ko sisi ga mutumin da ya ke mata barazana ba.
Da fari an soma tura sakon barazanar ne ga manajanta a ranar Laraba wanda kuma nan take ya sanar da ita da kuma adadin kudin da aka nema ko a wallafa bidiyon, kamar yadda BBC ,hausadailytimes na wallafa.
Ta kuma shaida cewa saurayinta ne a bisa kuskure ya soma ɗaura hoton a shafin sada zumunta kuma nan take ya goge, sai dai tuni mai yi mata barazanar ya yi sa’ar sauke bidiyon.
Tiwa ta ce a halin yanzu saurayinta na cikin damuwa.
Mawakiyar ta ce da farko ba ta ji dadin faruwar lamarin ba, amma dai kuma ba za ta amince a yi amfani da wannan damar wajen ɓata mata suna ko durkusar da ita ba.