Kannywood

Zuwa ga (matashin) ɗan jarida – Daga Abdulaziz Abdulaziz Deputy General Editor Daily Trust Akan Labarina

Barkanmu da war haka.
Tun jiya Asabar na ga ƴan uwa ƴan jarida, da masu sha’awar aikin da abokan ƴan jarida na ta kumfar baki kan yadda aka nuna aikin jarida a shirin wasan kwaikwayo na Labarina da ake shiryawa a tashar Arewa 24. Bisa ga duk bayanan da na gani, mutane na nuna rashin jin daɗin hantara da wulaƙanci da aka yiwa ɗan jarida a cikin shirin da kuma bashi kuɗin mota (brown envelope) da aka yi. Masu nuna rashin jin daɗi na gani an ci mutuncin sana’armu. Amma meye baƙo a abinda aka nuna?
Ba yau aka fara wulaƙanta ɗan jarida ba a Nigeria ta hanyar kyara da kallon raini ko ma abinda ya zarta haka. Amma yadda wasu abokan aikinmu da yawa suka mayar da aikin shi ne yake jawo wannan wulaƙancin domin duk wanda ya maida kansa ƙasƙantacce kuma mai kwaɗayi dole haka kowa zai gan shi kuma ya mu’amalance shi a haka. Wannan wulaƙanci kuwa yana da tushe, kuma yana da alaƙa da yadda masu aikin da yawa suke shigarsa ba tare da sanin muhimmancin aikin ba ma.
Ɗan uwa, ka kuwa san cewa ɗan jarida yana da sahalewar tsarin mulkin Nigeria domin ya zama mai sa ido kan yadda duk sassan gwamnati ke gudunar da aikinsu don cigaban ƙasa? Wannan ne yasa kamar alƙali ko jami’in tsaro, ana sa ran ɗan jarida ya kasance mai gaskiya da rashin tsoro da kuma yin aiki ba-sani-ba-sabo domin dai tabbatar da fito da gaskiya da kuma sa wa masu mulki ido akan tabbatar da sun sauke haƙƙin jama’a da ke kansu. Kai wakilin jama’a ne kuma jama’a sun baka amincewa shi yasa ma komai aka ji daga kafar yaɗa labarai mutane kan amince da shi.

Zuwa ga (matashin) ɗan jarida - Daga Abdulaziz Abdulaziz Deputy  General Editor Daily Trust Akan Labarina
Zuwa ga (matashin) ɗan jarida – Daga Abdulaziz Abdulaziz Deputy General Editor Daily Trust Akan Labarina

Don haka, wanda aka ɗorawa wannan babban nauyi yakamata a ce an kula da shi ta fuskar albashi sannan shi kuma ya kauda kai daga kwaɗayin abin duniya. To amma a nan ne gizo yake saƙar. Masu kafafen yaɗa labarai da dama basu damu da sauke haƙƙin ma’aikatansu a kansu ba. Gidajen jarida da dama basa biyan albashi, ko kuma suna biyan abinda ko sati guda ba zai ishi mutum ba. Wasu kamfanonin da suka san muhimmancin kula da ma’aikata domin yin aikin yadda ya kamata suna ƙoƙari sosai. Misali a kamfanin Daily Trust, 25 ga wata ake biyan albashi. Haka nan a shekaru 3 da wata 5 da na yi a Premium Times ba watan da ya taɓa ƙarewa ba tare da an biya albashi ba, baya ga tsarin inshoran lafiya da fansho ga ma’aikata. Wannan sauke nauyi da kula da ma’aikata yana sa jajircewa da kuma rage hangen abin hannun wani.
Abu na biyu shi ne kwaɗayi. Saboda yanayin aikinmu muna mu’amala da mutane masu hannu da shuni. Yawancinsu kuma suna da buƙatarmu domin su gyara kansu ko kuma su ɓata wani a don haka a shirye suke su “biya” domin buƙatarsu ta biya. A irin wannan yanayi abubuwa biyu ne a gabanka: Tsayawa akan gaskiya da adalci (kamar yadda aikin ke buƙata) ko kuma ka bi abin duniya.
Akwai waɗanda za su baka kuɗi “na mota” ba tare da yarjejeniyar ga abinda lallai zaka yi musu ba. A haka zaka ga kamar bashi da illa amma yana da ita, babba ma kuwa. Idan ka je taro ko ka yi hira da wani aka baka kuɗi to ba makawa an siye ƴancinka na rubuta labari bisa yadda yakamata domin kuwa ba zaka iya rubuta abinda ba zai yiwa wannan mutum daɗi ba, koda kuwa shi ne abinda jama’a za su so sani. Kamar yadda Bahaushe ke cewa, idan baki ya ci, ido zai ji kunya.
Amma idan baka ci kuɗin mutum ba kana da ƴancin ka yi labarin ka yadda ka so, koma ka ƙi yi gaba ɗaya. Bari in baka misali.
Kamar shekara uku da ta wuce akwai wani ɗan kasuwa da aka haɗa mu da shi, ni da Jaafar Jaafar akan cewa wani abokin kasuwancinsa ya cinye masa kuɗi. Mu ka haɗu ya yi mana bayani dalla-dalla. Labari ne duk ɗan jarida zai so ya samu har ma da takarda na yadda aka turawa wancan babban dan kasuwa kuɗaɗe. Da za mu rabu mutumin nan ya ce zai bamu kuɗi muka ce masa a’a. Ba yadda bai yi da mu ba amma muka ƙi. Har na fara rubutu labarin amma da muka samu ganin shi ɗaya mutumin muka saurare shi sai take muka gane cewa wancan ɗayan gaskiyarsa bata cika ba, ya tauye bayanai kuma kawai yana son a kunyata wannan abokin harkar tasa ne. Muna fitowa muka yanke shawarar haƙura da labarin, haka kuma muka bari. Da a ce mun karɓi kuɗin wancan mutum na farko da wataƙila dole haka zai yi amfani da mu mu ɓata sunan wannan ɗayan duk da cewa shi wancan ba cikakkiyar gaskiya yake da ita ba. Shi yasa a kullum zaman lafiyarka a matsayinka na ɗan jarida shi ne gudun abin hannun mai baka labari (source).
Baya ga waɗancan ginshiƙai guda biyu na san maganar ba ɗan jarida kuɗi tana kuma da nasaba da al’ada. Yawanci babba yana ganin abin kunya ne na ƙasa da shi ya haɗu da shi bai bashi komai ba. Don haka bawa ɗan jarida (wanda yawanci yaro ne matashi) “kuɗin mota” ya zama kamar karramawa ce irin ta al’ada, misalin irin wannan shi ne al’adar bada na goro ga ma’aikatan gidan abinci (restaurants) musamman a kasar America. Su abin kunya ne ma ka ci abinci baka ƙara wani abu ba akan kuɗin abincin domin kyautatawa ga ma’aikata. Da na tambaya a wata tafiya da na yi US sai aka ce min suna saka “tip” ne saboda yawanci ma’aikatan ba a biyansu da kyau don haka abinda suka haɗa a hannun kwastoma da shi suke ƙarawa a kan albashinsu. Amma kai da kanka na san zaka ce ai ba za a haɗa waiter na restaurant da kai da kake aikin bin bahasin mulkin jama’a ba. Sai dai kuma a ɗaya hannun kamar yadda ma’aikacin gidan abinci a Amurka baya samun kyakkyawan biya, haka ma yawancin ma’aikatan jarida a Nigeria ga kuma buƙatun rayuwa na yau da kullum. Idan haka ne, meye mafita? Akwai ta!
A matsayinka na ɗan jarida akwai hanyoyi samun halak da dama da zaka iya maida hankali a kai. Ga wasu shawarwari:
1. Haɗa aikinka da wani abu: Samarwa kanka wata mashigar kuɗi musamman a bangarorin da ke da alaƙa da aikinka. Misali zaka iya gwanancewa a aikin fassara, ko bincike (research) ko bin diddigi (investigation/due diligence), ko bada horo (training) wanda wannan zai iga kawo maka kuɗi mai tsafta lokaci zuwa lokaci. Idan ka iya fassara kana zaune ma wani lokaci aiki zai faɗo. Misali bara a aikin fassara guda ɗaya mun samu naira miliyan biyu. Haka nan idan ka fara nisa a aikin zaka iya shiga sana’ar horar da ma’aikata wadda a lakca na awa ɗaya kaɗai za a iya biyan ka daga N50, 000 zuwa N200,000. Akwai kuma aikin jan ragamar taro (MC) ko ɗaukar bayanan taro (rapporteur). Duk waɗannan damarmaki ne da ɗan jarida zai iya sa kansa a ciki domin samun ƙarin kuɗin shiga.
2. Talla (adverts): Wasu gidajen jaridun su kan hana masu ainahin aikin rahoto shiga neman talla domin gudun hakan ma zai iha sa ɗan jarida ya zama baya iya tsage gaskiya kan waɗanda suke bashi talla. Idan inda kake aiki basu da irin wannan matsayar, neman talla wata hanya ce da zaka iya samun ƙarin ƙuɗaɗen kashewa domin kana da kamasho a duk aikin da ka kawo.
3. Ƙulla alaƙa: Ka daure ka guji “biya” na nan take. Maimakon haka yi ƙoƙarin ƙulla alaƙa ta mutunta juna. Yawanci duk masu bada labarai (news makers) sun saba da cewa mu’amala da ɗan jarida sai ka tanadi kuɗi. Idan ka nuna kai na daban ne, nan da nan zaka jawa kanka mutunci da kuma mutuntawa. Maimakon kallonka a matsayin wani da aka haye shi domin yayi aiki a biya shi, zai kalle ka a matsayin mutum. Da irin wannan halin sai ka ga Allah ya haɗa ka da mutumin da zaka amfane shi fiye da kuɗin da zai baka a wulaƙance, domin ita rayuwa ba komai ba ne kuɗi. Akwai abu da yawa da yafi kuɗi wanda kuma mu’amala mai kyau ce kaɗai zata iya baka.
Akwai wani mutum da ya nemi kan wani labari mai zafi da yake son duniya ta sani. Da muka haɗu bayan ya gama bani labarin sai ya ce zai bani takardu idan mun sake haɗuwa. Na same shi kuwa a gida amma da zai bani takardun sai cewa “Me zan samo maka to?” sai na ce “Kamar me?” Ya ce “Ah, abinda za ka riƙe mana don ka samu ƙwarin guiwar aiki” na ce masa “bana buƙatar komai”. Sai ya cewa ya yi gaskiya hankalinsa ba zai kwanta ya bani komai da komai ba idan bai bani kuɗi ba domin waɗancan za su iya bani kuɗi mai yawa don kar a yi labarin. Sai na ce masa “Ai na ɗauka yarda ce ta sa ka neme ni. Idan baka yarda da ni ba to ma bari kawai”. Faɗar mutumin yai ajiyar zuciya ya kawo documents ya bani. Na je na cigaba da aiki na yadda yakamata. Wannan abin ya ja min mutunci ƙwarai a wajen mutumin nan kuma da wta buƙata ta taso, ba tare da na roƙe shi ba hak ya bugi jikinsa da ɗanyen kara ya yi min abinda ya ban mamaki. Wannan shi ne amfanin ƙulla alaƙa mai kyau.
Ya kai ɗan jarida a ƙarshen duk wannan batun ka sani kai ne babban alƙalin kanka domin lokuta da dama da sanda za a nemi siye imaninka da mutuncinka daga kai sai mai baka kuɗin nan, sai Allah. A irin wannan yanayi conscience dinka shi ne linzamin ka. Aikin nan nauyin al’umma ne da amanarsu akan dukkaninmu. Ba kuwa babbar cin amana irin a haɗa baki da kai a faɗawa mutane abinda ba haka ba, ko kuma ka zama karen farauta. Haka kuma duk mutumin da alaƙarku ta kasance ta “kuɗi hannu” ce ka tabbatar ba zaka taɓa yin kima a wurinsa ba. Zai kasance tsakaninka da shi sai yana da buƙatarka idan ka zo ya “biya” ka ka yi masa abinda yake so. Shikenan.
Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya faɗa: Ka guji abin hannun mutane, sai mutane su so ka.
Allah ya datar da mu.
Naka
Abdulaziz Abdulaziz

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA