Kannywood

Zan gina cibiyar harkar finafinan Hausa a Nasarawa – Gwamna Sule

Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya na gabatar da jawabi ga tawagar ta MOPPAN a Gidan Gwamnati da ke Lafiya jiya
Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya na gabatar da jawabi ga tawagar ta MOPPAN a Gidan Gwamnati da ke Lafiya jiya
Hoto: Fim magazine

GWAMNAN Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, ya bayyana ƙudirin sa na mayar da jihar cibiyar gudanar da harkokin finafinan Hausa saboda gudunmawar da masana’antar Kannywood ke bayarwa ga cigaban ƙasa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), waɗanda su ka ziyarce shi a Lafiya a ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na ƙasa, Dakta Ahmad Muhammad Sarari, a jiya Talata, 22 ga Satumba, 2021.
A takardar sanarwa ga manema labarai da ya turo wa mujallar Fim, kakakin ƙungiyar, Alhaji Al-Amin Ciroma, ya ambato gwamnan ya na faɗin cewa, “Ko shakka babu ina alfahari da matasa masu shirya finafinai, musamman ma da ya kasance su na amfani da wannan damar da Allah ya ba su har su zama wasu fitattun mutane a cikin al’umma.”
Ya kuma ce, “Ina matuƙar alfahari da yadda na ke ganin masu shirin fim, ko kuma kowace sana’a, musamman ma da su ke amfani da damar su har su zama wasu mutane da ake alfahari da su.

Karanta kuma  Martani: Rikici tsakanin ‘yan fim da ‘yan jarida a kan ‘Labari Na’
Gwamna Sule (a dama) ya na miƙa wa shugaban MOPPAN Dakta Sarari garkuwar karramawa
Gwamna Sule (a dama) ya na miƙa wa shugaban MOPPAN Dakta Sarari garkuwar karramawa Hoto :fimmagazine

“Amma don na ga ɗan mai kuɗi ya zama wani a rayuwar sa, hakan bai cika burge ni ba, domin matashin da ke da ƙaramin ƙarfi, sai ya ci kwakwa sannan ya zama fitacce.
“To, shi ya sa na ke son tallafa masu, saboda duk matsayin da su ka taka a rayuwa, ba za su taɓa mantawa da kai ba.”
Ya ƙara da cewa ƙofar sa a buɗe ta ke ga dukkanin masu shirin fim na Kannywood.
Haka kuma gwamnan ya kuma yaba da tsare-tsaren MOPPAN, inda ya amince cewar zai ɗauki nauyin babban taron ƙungiyar da za a yi nan da makwanni kaɗan.
Sule ya ce, “Na ji daɗi matuƙa da ganin fuskokin da na ke jin daɗin ganin su a cikin finafinai. Hakan ta sa na ke tabbatar maku da cewa zan yi iya ƙoƙari na wajen samar da cigaban da duk ake buƙata, matuƙar ku ma za ku jajirce.

Membobin MOPPAN da jami’an gwamnati a wajen taron
Membobin MOPPAN da jami’an gwamnati a wajen taron Hoto : fimmagazine

“Saboda haka, za mu ɗauki nauyin taron ku da ku ke shirin yi da yardar Allah.”

Karanta kuma  Naziru Sarkin Waƙa ya hayaƙa ‘yan jarida

A kan batun bayar da horo ga ‘ya’yan masana’antar kuwa, gwamnan ya tabbatar da cewa za a ba wa MOPPAN damar haɗin gwiwa da makarantar koyar da fim ta Tarayya (NFI) da ke Jos domin horas da masu shirya finafinai na Jihar Nasarawa.
Game da samar harkar finafinai gami da samar wa MOPPAN da katafaren ofis kuwa, gwamnan ya amince da buƙatar a nan take.
Gwamnan ya ƙara da cewa ya na neman haɗin gwiwar MOPPAN da ƙwarewar ta wajen ƙarasa da bunƴasa cibiyar shirya finafinai ta zamani a Farin Ruwa, wato ‘Farin Ruwa Film Village’ da gwamnatin sa ta fara.

Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya na gabatar da jawabin sa
Shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari, ya na gabatar da jawabin sa Hoto: fimmagazine

Tun da fari dai, a cikin jawabin sa, sai da shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Sarari, ya bayyana wa Gwamna Sule muhimmancin masana’antar finafinan Hausa da tasirin ta a cikin al’umma da kuma yadda Kannywood ta ke bayar da gudunmawa ta fannin wayar da kai gami da samar wa matasa da aikin yi.
Shugaban ƙungiyar ya ce, “Ko shakka babu Kannywood ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, za ta yi kyakkyawan haɗin gwiwa da gwamnatin Jihar Nasarawa domin haɓaka harkokin finafinan Hausa tare da wayar da kan mutane a kan alfanun haɗin kai da kyakkyawar zamantakewa.”

Karanta kuma  Rasuwar Ahmad Tage asara ce ga Kannywood, inji MOPPAN da ‘yan fim

Domin samar da kyakkyawan yanayin haɗin gwiwar, gwamnan ya karrama ƙungiyar da lambar yabo, a yayin da ita ma MOPPAN ta maida biki ta karrama shi a matsayin ‘Jagoran Harkar Finafinai na Nijeriya.’

Teburin shugabanni a taron
Teburin shugabanni a taron Hoto : fimmagazine

Taron dai ya samu halartar wasu daga cikin shugabannin MOPPAN na ƙasa, waɗanda su ka haɗa da ma’ajin ta na ƙasa, Alhaji Bala Kufaina, da kakakin ta, Alhaji Al-Amin Ciroma.
Sauran sun haɗa da darakta Ishaq Sidi Ishaq, memba a kwamitin gudanarwa na MOPPAN, Dakta Ahmed S. Bello, Sakataren Kwamitin Zaɓen MOPPAN, da kuma darakta Kamal S. Alƙali.

Wani sashe na mahalartan taron
Wani sashe na mahalartan taron Hoto: fimmagazine

Har ila yau, akwai jarumai kamar Malam Abdullahi Ƙarƙuzu, Malam Magaji Mijinyawa, Hajiya Hadiza Muhammad (Hadizan Saima), Amina Amal, Bilkisu Abdullahi da kuma tawagar ‘yan wasan Jihar Nasarawa.
Daga :Fim magazine

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button