Labarai

Yadda Ake Zaba Wa ‘Ya Mace Miji Ana Haihuwarta A Kabilar Eggon

Yadda Ake Zaba Wa ‘Ya Mace Miji Ana Haihuwarta A Kabilar Eggon
Batun aure a wannan kabila kuwa, a iya cewa tun ranar gini, ranar zane. Domin kuwa, yadda al’adarsu ta shimfida shi ne cewa, idan aka haifi yarinya ba tare da bata lokaci ba akan ayyana wanda za a hada su aure idan sun girma. Wannan ne ma ya sa aka ce ba kowace mace ya kamata ta taba jinin mai haihuwa ba sai wadda ta kasance akwai dangantaka ta jini a tsakaninta da mai haihuwar. Bayan iyaye sun shaida wanda aka sanar da sunansa a kan za a hada su aure da jaririyar idan dukkansu biyu suka kai minzili, haka za a ci gaba da sanya musu ido tare da aiwatar da duka abubuwan da gargajiyarsu ta gindaya, musamman ma daga bangaren namijin zuwa ga yarinyar da ma iyayenta. A kalla shekara guda kafin auren, haka saurayin zai yi wa iyayen yarinya hidima ta hanyar hada kan abokansa a tafi gonan iyayen yarinya a zabga musu aiki da dai sauran abubuwan kyautatawa.
Kamar yadda hausaleadership na ruwaito bayan iyayen yarinya sun gamsu da dukkan abin da surukin nasu ya yi, sannan ne za su yi masa sammaci tare da sanar da shi cewa an ba shi auren wance.
Dagan an saurayin zai tafi ya shammaci yarinyar a duk inda ya ganta kawai sai ya sungume ta sai gidansu, shi kenan aure ya tabbata. Su kuwa iyayen yarinya a wannan lokaci, idan suka ji shiru ‘yarsu ba ta dawo gida ba sun rigaya sun san abin da ya faru. Bayan haka ne sai kuma  a shiga biki.
A wannan kabilar, maza na sakin mata haka ma matan na sakin mazansu idan bukatar hakan ta taso.
Suna kyamatar zina matuka saboda bata sunan zuri’a da kuma kuma bata wa ababen bautarsu rai, hakan ya sa duk wanda aka kama da laifin zina  nan take ake hukunta shi sannan kuma a ci shi tara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button