Tarihin Sir Ahmadu Bello Sardauna Sokoto
Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wanda na daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.
Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina.
Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.
A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi.
Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.
Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.
Ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966.
Sannan ya jagoranci jam’iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun ‘yancin kai.
Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista.
Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.
An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji ‘yan kabilar Ibo suka jagoranta.
Ga bidiyon nan domin karin bayyani