Kannywood

Shin isowar Afakallah ce ta janyo ficewar Nabraska da Oscar daga zauren taron Kannywood da NDLEA?

Shin isowar Afakallah ce ta janyo ficewar Nabraska da Oscar daga zauren taron Kannywood da NDLEA?FITACCEN jarumi Mustapha Nabraska ya bayyana dalilin da ya sanya shi da babban darakta Sunusi Oscar442 su ka fice daga zauren taron haɗin gwiwa tsakanin masana’antar Kannywood da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA).
An yi taron ne don tattaunawa kan yadda za a samo bakin zaren ta’azzarar da matsalar shaye-shaye ta yi a Jihar Kano, kuma haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa (MOPPAN) ita ce ta shirya shi tare da haɗin gwiwar NDLEA.
An yi taron a jiya Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a harabar gidan talbijin na ‘Kannywood TV’ da ke Kano, mallakar shugaban MOPPAN na ƙasa, Dakta Ahmad Sarari.
To amma ficewar Nabraska da Oscar442 daga zauren a daidai lokacin da ake tsakiyar gudanar da taron ta haifar da zargin cewa sun yi haka ne saboda shigowar shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah).
Kamar yadda fim magazine na ruwaito tun da fari, jarumin da daraktan, waɗanda su ka yi shiga ta fararen kaya da jar hula irin ta magoya bayan rundunar adawa ta Kwankwasiyya, sun samu matsuguni a kujerun zama a baya, inda su ka riƙa ɗan tattaunawa a tsakanin su.
Can, jim kaɗan bayan da Afakallah ya iso zauren, Nabraska ya tashi ya je teburin manyan baƙi ya miƙa wa kowa hannu su ka gaisa, to amma sai ya tsallake Afakallah.
Gama gaisawar tasa da manyan baƙin ke da wuya kuma, sai aka ga shi da Oscar442 sun fice daga ɗakin sun yi tafiyar su.
Wannan abu ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu daga cikin mahalarta taron, inda su ka ce lallai lamarin ya na da nasaba da zuwan shugaban Hukumar Tace Finafinan.
Sanin kowa ne ana tafka tsama a tsakanin shugaban hukumar da waɗannan jigajigan ‘yan fim biyu, wadda ta kai Oscar442 ya janye daga harkar shirya fim a Kano.
Su biyun su na daga cikin manyan ‘yan Kannywood da ke bin siyasar tsohon gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hukumar Tace Finafinan ta taɓa kama daraktan ta maka shi a kotu, inda daga can aka kai shi gidan waƙafi a kan tuhumar sakin wata waƙa da ya yi wa daraktin ba tare da izinin hukumar ba.
Kwanan nan a hirar sa da mujallar Fim, daraktan ya zargi Afakallah da musguna masa saboda bambancin ra’ayin siyasa. Amma Afakallah ya sha ƙaryata zargin.
A dangane da abin da ya faru jiya a wajen taro, mujallar Fim ta tuntuɓi Nabraska don jin ta bakin sa kan zargin da ake yi cewa sun fice daga taron ne saboda Afakallah.
Jarumin ya musanta zargin da cewa, “Babu rami me ya kawo maganar rami?” Ya ce wani uzuri ne ya sanya su ka tashi daga wurin taron.
A cewar sa, “Mu na da uzurirrika da yawa, kuma ka ga tunda an gayyace mu mun je, kuma ga uzirin mu, dole mu je mu gaisa da jama’a don a ga cewa mun amsa gayyatar da aka mana.
“Sannan kuma maganar da ake faɗa na cewa don mun ga wani ne, mu ba mu kula da shi ba domin ba ta tashi mu ke ba. Don haka wannan zargin ba haka ya ke ba.”
Sai dai Nabraska bai ce uffan ba kan dalilin sa na ƙin gaisawa da Afakallah.
Daga: fimmagazine

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA