Kannywood

Sakon mu ya fi na Malamai isa ga al’umma – Limamin Mata Ado Gwanja

Ado Gwanja – Sakon mu ya fi na Malamai isa ga al’umma
Ado Gwanja – Sakon mu ya fi na Malamai isa ga al’umma

Wani shafi mai suna Punch Hausa a dandalin Facebook ya kawo labarin wata hira da suka yi da mawaki kuma jarumi Ado, a cikin hirar jarumin ya bayyana cewa sakon su masu harkar nishadi yafi saurin isa ga al’umma fiye dana Malamai, inda ya bada hujjojin sa.
Sai dai kuma wannan lamari ya zama abin muhawara a shafin, inda wasu ke ganin batun na Ado Gwanja akwai kamshin gaskiya a ciki, wasu kuma suke ganin cewa soki burutsu ne, inda suke ganin bai kamata ya kwatanta Mawaka da Malamai ba.Ga dai yadda rahoton yake:
Sakonmu Yana ishewa Fiye Dana Malamai Cewar Mawaki Ado Gwanja.
Ana Yarda Damu Ana Kallonmu Kuma Ana Sauraronmu Fiye da Yadda Akewa Malamai Sabida A halin Yanzu Mutane Sunfi karkata Ga Harkar Nishadi Fiye da jin Wa azi,Sabida Haka Mafita Kwai shine Adaina Kyamatar Harkar Malamai sushigo ciki Domin A Musuluntar da Harkar Yadda zata Dace Da Addini Da Kuma Al adarmu, cewar Gwanja.

Ado Gwanja

Haka Ilimin Boko Malamanmu Na Wancan loakaci da Kuma Mutanen kirki suka dinga kyamatarshi Akabar Harkar Amatsayin kafirci sai Yazamana Mafi yawan Wadanda suke Ilimin a Wancan loakacin Basuda Ilimin addini saigashi a yanzu susuke Mulkar Alumma.
Haka ma Maganar Film bilage Maimakon Abari Ayishi A Kano inyaso sai ashigo da Malamai da Hisbah cikin lamarin gudun kar Adinga Wani Abu da Bai dace ba Amma sai aka Hana gabadaya to idan akayishi a wata jihar Makociyar Kano fa kaga Abinda ake gudu Dole shizaifaru Maimakon Ayishi a kano A Musuluntar Dashi kaga aka yishi a kaduna baza a Musuluntar Dashi ba Kuma Dole zai shafi Yan Cewar Gwanja a wata Hira da yayi da punch Hausa

Rahoton wanda suka wallafa ranar 6 ga watan Satumbar nan ya jawo kace nace matuka, to sai dai kuma lamarin ba a iya nan ya tsaya ba domin kuwa, 8 ga watan Satumba sun sake wallafa wani rahoto, inda suka bayyana cewa jarumin ya ce, inda suka ce da ace sana’ar ta su da lalata tarbiyya take da tuni yanzu babu inda ake zaune lafiya.
Ga dai rahoto kashi na biyun:
Da Muna Sana ar Mune Don Lalata Tarbiyya Da Yanzu Zamanlafiya Ya Gagari Uban kowa A Nigeria, Cewar Ado Gwanja,?????️.
Kaso biyu,2 cikin Uku ,3 Na Alumma Suna bibiyarmu Kuma suna Gamsuwa Da Duk Wani Abu Damukeyi To Wannan Tasa Muke taka tsantsan Wajen Yin FinaFinai da Wakokin Damuke.
Sau da yawa zaka ga
Mutum har kuka yake Yayin da Ya Kalli Wani Film Mai ban tausayi kokuma Kaga Mutum Yana jin Haushin Actor na Film kawai Sabida Roll din da akasa Acton zakaga Roll ne Na Mugunta iya Wannan Zaisa Agane irin imanin Da Mutane sukaimana Cewar Ado Gwanja.

Jama’a dai na cigaba da bayyana ra’ayoyin su kan wannan batu, ba tun yau ba ‘yan masana’antar ta Kannywood ke shan suka daga al’umma akan batun cewa da wasun su ke yi cewa tarbiyya suke koyarwa, inda al’umma suke kalubalantar su kan wannan lamari.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

  1. Eh mun gamsu da cewa saƙonku ya dara na malamai isa ga al’umma bisa irin yadda kuke amfani da duk wani abu mai fincikar zuciya mai rauni
    Amma sakon malamai yafi naku muhimmanci gami da yiwa rayuwar dan Adam garan-bawul
    Batun cewa malamai su tsoma baki akan harkar domin a musuluntar da ita muna goyon baya
    Kuma meyasa kace amusuluntar da harkar ashe!!kasan ta sabawa ruhin tafarkin Muslunci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button