Kannywood

Nayi Babbar Sa’a A shiga Harkar Fim – Fati Shu’uma

Nayi Babbar Nasara A shiga Harkar Fim - Fati Shu'uma

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood Fati Abubakar, wacce aka fi sani da sunan Fati Shu’uma, ta bayyana irin sa’ar da take da ita ta shiga harkar fim, wanda hakan ya sa ba ta sha wata wahala ba, ta samu shiga kuma lokaci guda ta zama fitacciyar jaruma.Nayi Babbar Nasara A shiga Harkar Fim - Fati  Shu'umaFati Shu’uma ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, in da ta ke cewa:
” Gaskiya ina kallon kaina a matsayin wacce ta yi sa’ar shiga harkar fim, domin na shiga harkar fim ban yi ko sati biyu ba aka yi mun fim, kuma na zama Jarumar fim kafin wata biyu duk in da na shiga ana kira na, saboda an ga tallar fim din, ka ga ba kowacce jaruma ke samu irin wannan sa’ar tawa ba. “Inji ta
Dangane da matsala kuwa mun tambaye ta ko ta samu wata matsala.?
Sai ta ce ” Eh na samu matsala, domin kuwa tun da zan je na ga yadda a ke yin fim din “Ga ni ga ka”, sai kanen Baba ta ya yi ta fada ya ce, don me ya sa na je? Ka san yadda mutane su ke daukar harkar fim. Shi ya dauka ko zan je na tare ne a gidan karuwai na zauna, amma daga baya sai ya fahimta ya bar ni. ” a cewar ta
Daga karshe Fati Shu’uma ta yi kira ga abokan sana’ar ta su rinka kiyaye rayuwar su da kuma yin mu’amala da mutane domin su na daban ne saboda duniya ta san fuskar su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA