Labarai

Na yi imani da Allah ko shi Isa Ali Pantami ya san bai cika ƙa’idojin Farfesa ba – Dakta Auwal Mustapha Imam

Wani Malamin jami’ar gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi a jihar Kebbi, Dakta Auwal Mustapha Imam, da ke Najeriya ya ƙalubalanci hukumomin jami’ar fasaha ta gwamnatin tarayya da ke birnin Owerri da ke jihar Imo akan ƙa’idojin da ta bi wajen baiwa ministan sadarwa Isa Ali Pantami muƙamin Farfesa.
Dakta Auwal Mustapha Imam ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na facebook mai taken ‘KYAUTAR FARFESANCI‘ wanda labarai24 sunka wallafa a shafinsu
A cikin rubutun Malamin jami’ar ya yi ikirarin cewa ko shi kan da Dakta Isa Ali Pantami ɗin ya san wannan Farfesa da aka ba shi ya saɓa da ka’ida da sharadin da ake bi wajen bayar da shi.
Ga dai rubutun Dakta Auwal Mustapha Imam kamar haka:

Sheikh Dr. Isa Ali Pantami
Na yi imani da Allah ko shi Isa Ali Pantami ya san bai cika ƙa’idojin Farfesa ba – Dakta Auwal Mustapha Imam

“Ko a lahira ba aikin mutum ke shiga da shi Aljannah ba, Rahamar Ubangiji ne kawai. Amma kyautatuwar aiki alama ce ta samun Rahamar Ubangiji. A duniya ma haka, ba dagewar mutum ko ƙoƙarinsa ne ke sa ya samu duniya ba. A ah, kawai ikon Ubangiji ne da rabo. Shiyasa sai ka ga wani ya fi ka dagewa wurin nema amma ka fi shi samu. Allah ya ce “…Mu ne muke kasa arziki tsakanin mutane wani ya fi wani.” Idan Allah ya ɗauka arziki ya ba waninka, dole ka haƙura ko da kuwa ka fi wanda aka ba zafin nema.
Haka abin yake ko a makaranta, za ka ga wasu sun fi kowa dagewa a karatu, amma Allah sai ya ba wanda bai kai su dagewa ba nasara a kan su. Haka a wuraren ayyuka, wani za ka ga ya kamata a ce an ba shi query saboda wasa da aiki, amma kwatsam sai Allah ya yi ta bashi ɗaukaka fiye da kowa. Ƙoƙarin mutum da dagewa wurin nema hanya ce da ke tabbatar da samu, amma ba a wa Allah dole.
A lokacin karatu na na Ph.D, na dage sosai don in gama da wuri, daga baya na fahimci nasarar karatun Ph.D ba kawai a dagewa bane, akwai ikon Allah a ciki. A sannu sai ga taimakon Ubangiji na yadda za a gama. Duk mai Ph.D da ke koyarwa a jami’a babban burinsa shi ne ya ga wata rana ya zama Professor. Kuma zama Professor ba kamar digiri bane da ake iya kyautarsu; sai mutum ya yi aikin koyarwa kuma ya yi ta bincike bincike.
Kwatsam sai Malaman jami’a suka ji wai Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami ya zama Professor a jami’a ma da bai san ina azuzuwan ta suke ba. Dole hakan ya jawo cece-kuce. Da a ce digirin girmamawa (Honorary doctorate degree) ne aka bashi ko guda dubu ne babu wanda zai yi magana. An jefi masu magana a kan wannan professorship ɗin da cewa hassada suke wa Dr. Pantami.
Ni a gani na ba hassada bace. Daman ai akwai wata nunanniyar hassada da duk mai Ph.D ke da ita; muna jin haushi idan an kira wanda bai yi Ph.D ba da Dakta. Gani muke kamar mu kaɗai ya kamata a kira da Dakta saboda wahalar da muka sha. Masu irin wannan tunanin ko ai ya zama wajibi su ji ba daɗi idan kwatsam aka ce wanda bai yi komi ba a koyarwa da bincike wai ya zama Farfesa.
Ana wannan irin ƙorafin ne ba don hassada ba, sai don kare martabar Farfesanci. Idan aka yarda da haka kuma aka bari abin ya cigaba, wata rana za a riƙa kai wa jami’o’i kuɗi ana sayen Farfesanci yadda ake sayen digirin girmamawa. Babban abin tsoron ma shi ne, za a zo lokacin da Malaman da suka kasa zama Farfesoshi za su riƙa shiga siyasa da neman muƙami domin cimma burinsu na amfani da muƙamin siyasa domin neman Farfesanci
Na yi imani da Allah, ko shi Farfesa Isa Ali Pantami ya san ƙa’idojin zama Farfesa, kuma ya san bai cika waɗannan ƙa’idojin ba. Idan ni ne shi, Wallahi ba zan amsa ba, kuma ba zan yarda a kirani da Farfesa ba don ban zama ba. Sanda na je Malaysia kafin in kammala karatuna, kunya nake ji idan an kira ni da Dakta
Amma yanzu da na wahala na samu, haushin mutum nake ji idan bai ce min Dakta ba. Me zai hana Farfesa Pantami ya yi koyi da irinsu Dr. Bala Usman da sauran mutanen kirki da suke gujewa lambar yabon da bata kamace su ba. Ina kira ga Farfesa Pantami da ya taimakemu ya mayar da wannan sunan ya amso abinda ya ba jami’ar ko ya bar musu kyauta. Idan kuma bai basu komi ba, to ya ki tsoron Allah ya rubuta musu cewa bai fa dace da zama Farfesa ba, saboda haka yana godiya da karramawa.

Auwal Mustapha Imam, B.Sc. M.Sc. (BUK), Ph.D. (UTM), Malami ne a jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke jihar Kebbi. Federal University Birnin Kebbi, Nigeria

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button