Kannywood
Na ajiye jar hula domin ba gadata aka yi ba-Naburuska
Advertisment
Ɗan wasan Hausar nan Mustapha Badamasi Naburaska ya ce, ya cire jar hula ya rungumi tafiyar Gwamna Ganduje.
Da yake zantawa da Freedom Radio a daren Asabar ya ce, ya cire jarhula domin ba gadarsa a ka yi ba.
Naburaska ya ƙara da cewa da haƙoransa 32 aka ganshi, don haka duk wanda zai taimaki sana’arsu shi ya ke yi.
“A duk Najeriya in ka cire Legas babu inda Gwamna yake zuba ayyuka kamar Kano, mu muke yawo mun je kuma mun gani”.