Uncategorized

Mu ƴan fim ba Malamai ba ne, sai dai muna faɗakarwa – Falalu Ɗorayi

Mai bada umarni kuma mashiryin fina-finai a masana’antar Kannywood Falalu Dorayi ya ce su ba malamai ba ne sai dai su na fadakarwa.
Falalu Dorayi ya bayyana haan a zantawar sa da Freedom Radio.
Dorayi ya ce “dukkanin mu daliban neman ilimin addinin musulunci ne, domin kuwa ni ma dalibin Dakta Ahmad ne kuma dalibin marigayi Shiekh Ja’afar Mahmud Adam ne”.
“Harkar fim ce ta hana ni ci gaba da zuwa guraren da ake wa’azi ko kuma makaranta, kuma babban abinda ya ke hada mu rigima da malamai bai wuce a kira da sunan muna wa’azi a fina-finan mu ba” a cewar Falalu.
Ya kuma ce, fim wani yanki ne na aika sako ga al’umma a aikace kuma cikin hikima don haka yan fim ba malamai ba ne.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA