Kannywood

Mawaƙi Naziru ya sa an kama matashin Mawaƙi Yarima El-musty

Mawaƙi Naziru ya sa an kama matashin Mawaƙi Yarima El-musty
Yarima El Musty Mai waka

‘Yan sanda a Katsina sun kama tare da tsare wani matashin mawaƙi mai suna Mustapha, da aka fi sani da ‘Yarima El-musty’.
Bayanan da DCL Hausa ta tattaro daga wani makusancin ‘El-Musty’ sun ce an kama Mustapha a daren Lahadi inda yake tsare a hannun ‘yan sanda.
Makusancin, da ya nemi a sakaya sunansa, yace Mawaƙi Naziru, na zargin Mustapha da amfani da sunansa wajen damfarar mutane, zargin da mafi yawa daga cikin abokan Mustapha suka musanta. Wasu zarge-zarge da makusancin ‘El-Musty’ yace ana yi, hada buga waya da sunan cewa Naziru mai waƙa ne, yana neman take mako, ya yi hatsari ko wata bukata ta gaggawa.
Matashin Mawaƙi Mustapha Abubakar
Sai dai makusantan Mustapha sun ce, ‘sam’ wannan zargi ba gaskiya bane, don kuwa Mustapha baya da wannan hali ko alama, har ma suka ce, ya kamata Naziru Mai waƙa ya tabbatar da gaskiyar abin da yake faruwa kafin daukar wannan mataki.
Mawaƙi Naziru ya sa an kama matashin Mawaƙi Yarima El-musty
Yarima el Musty Kenan mai waka

Bayanai dai sun ce, sai Naziru ya bar Kano, ya zo Katsina, sannan a iya sanin makomar Mustapha dake tsare a hannun ‘yan sanda.
Mustapha, da aka fi sani da ‘Yarima El-musty’ na salon waka da murya irin na Mawaki Naziru da wasu ke ganin kamar akwai kyakkyawar alaka tsakanin su da har ta kai ga yana kwaikwayonsa.
Saurari kadan daga cikin wakokin yarima elmusty gata nan kasa.

Isah Bawa Doro, na daga cikin makusantan ga masu harkar fim na Hausa, da DCL Hausa ta tuntube shi game da batun, yace baya da cikakkiyar masaniya game da abin da ke faruwa, amma dai ya san ana samun ire-iren wadannan matsaloli musamman ga fitattun mawaka, ta yadda wani zai amfani da sunansu ko muryarsu domin ya damfari fitattun mutane.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA