Masha Allah : Ba’a Taba Samun Dan Izalah Alhusunnah A Harkar Ta’addanci Ba A Nigeria – Sheikh Kabiru Gombe
A daidai Lokacin da Nageriya ke fuskantar barazanar ta’addanci kala-kala A cikin wani Sabon bidiyon wa’azin Sheikh Kabir Gombe Wanda Jaridar Mikiya ta bibiya Wanda suka gabatar a garin Tour ta jamhoriyar kasar Niger an jiyo malamin Yana magana akan mahimmancin Sunnah da Aqeeda da yadda Sunnah ta mamaye kasashen Africa aciki ne aka jiyo shehun malamin yana cewa masu saka bakaken Hula akeda ce matasa ne aka ‘diba aka cusa masu suna saka bama-bamai a Kan hanya Kuma suna tsammanin Allah zai basu lada kuma dasa masu akayi Kuma su wanene? Matasa ne inji Malam Kabir Gombe.
Har’ila yau malamin ya kara da cewa duk matashin da malaman sunnah suka tarbiyance shi ba zaka sameshi cikin harkokin ta’addanci ba mun auna tare da bincike a Nageriya cewa ‘dan izalah daya Sha Sunnah ya koshi kwara ‘daya bamu taba samu a cikin harkar ta’addanci ba Kuma mun kalubalanta cewa idan akwai shi a kawo Mana shi mu ganshi, malamin yace duk wanda ka ganshi a cikin harkar ta’addanci Yan ba kungiya ne Suka cusa masa.
wannan wa’azi na sheikh Kabir Gombe na zuwa ne a daidai Lokacin da Nageriya musamman arewacin Nageriya ke fama da barazanar ta’addanci lamarin da yafi tsamari a jihohin Borno yobe adamawa Benue taraba da Jos sai arewa maso yamma dake fama da hare haren Yan bindiga masu garkuwa da mutane Wanda akasarinsu matasa ne kawo yanzu Babu wani bincike daga Gwamnati Wanda ta fitar cewa lamarin ta’addanci na da alaka da wata kungiyar addinin Nageriya.
Malam yayi wannan maganar ne domin kira ga matasa da su san cewa suna da martaba da daraja a wajen ayyukan alkhairi, kuma dasu ne ake amfani wajen aikin ta’addanci Allah yasa mudace amen.
Ya ku matasa kusani cewa a koda yaushe ana so ku zama gaba gaba a wajen aikin alkhairi domin shi ke nuna cewa za’a dade anayi.
Ga bidiyon nan domin sauraren wa’azin malam a kasar Niger.