Labarai

Luguden wuta ga ‘yan ta’adda ba shi ne mafita ba – Dr Ahmad Gummi

Luguden wuta ga ‘yan ta’adda ba shi ne mafita ba - Dr Ahmad Gummi Babban malamin addinin Musulunci a arewacin Nijeriya Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kai wa yanzu a kan masu aikata miyagun laifuka da ‘yan fashi da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.
Majiyar DCL Hausa ta Daily Nigerian ta ce Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan ‘yan bindiga a dazukan Zamfara.
Sanarwar, mai taken: ‘Zamfara: The Flaring of Crisis’, ta jaddada cewa matakin soji kan masu aikata miyagun laifuka “ba mafita bane ko hikima” inji shehin malamin.
 

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button