Ina son Nafi Kowace Jaruma Daukaka A Kannywood – Jaruma Nuraiwa Abdullahi
A kowanne lokaci ana samun Sabbin jarumai da su ke shigo wa cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood, kuma duk wanda ya shigo cikin masana’antar, babban burin sa bai wuce a ce ya yi suna ya zama fitaccen jarumi ba.
Don haka, Sabuwar jaruma Nuwaira Abdullahi, wadda ‘yar asalin garin Jos ce kuma ba ta dade da shigo wa cikin harkar ba, Amma dai ita ma burin ta bai wuce ta samu dama ta yi fice a cikin masana’antar ba.
Jarumar wadda ta fara fito wa a cikin wani sabon fim mai suna Gona Gari a shekarar 2020, kuma ta yi kokari sosai a fim din, wanda hakan ya sa a ke ganin nan gaba kadan Idan ta samu dama to burin ta zai iya cika.
A lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, jaruma Nuwaira Abdullahi ta bayyana dalilin ta na shigo wa harkar fim da cewa
“ina son duniya ta sanni na yi fice a cikin harkar fim, don haka ina da burin na sha gaban kowacce jaruma a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood. Domin su ma mata ne kamar ni, don haka ina da karfin gwiwar da zan taka duk wani matakin da wata mace za ta taka, don ta yi fice a duniya. ” Inji ta
Ta Kara da cewar” Na san daukaka ta Allah ce, kuma shi ya ke bayarwa, don haka ina da kyakyawan fata Nima Allah zai ba ni daukakar da zan cimma burina, na ganin na sha gaban duk wata Jaruma da take cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood. ” a cewar ta.
A karshe jaruma Nuwaira Abdullahi, ta yi fatan alheri ga dukkan wanda ya taimaka mata, don ganin ta cimma burin ta na ganin ta sha gaban duk wata Jaruma.