Addini

Hukuncin Aure – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Hukuncin Aure - Sheikh  Aminu Ibrahim Daurawa A jumlace malamai sun kasu kashi uku dagane da hukuncin aure :
1- Su ne waɗanda suka tafi akan wajabcin yin aure sau ɗaya a rayuwa.
A ra’ayin waɗannan malamai Idan mutum ya yi aure sau ɗaya to ya sauke nauyin dake kansa. Ya yi aiki da da hadisan da suka ce ayi aure.
2- Malamai na biyu su masu ra’ayin cewa shi aure mustahabbi ne, wato ba wajibi ba ne. In ka yi aure za ka samu lada. Idan baka yi ba kuma ba ka da alhak i- amma da sharaɗin mutum zai iya tsare mutuncin kansa.
Ba zai zamo mai kalle kallen matan mutane ba har ya kai ka ga sha’awarsu ba,.
Ba kuma zai aikata zina ba ko danginta ko ya dinga bin wasu hanyoyin da suka saɓawa shari’a wajen biyan buƙatarsa ba. Kamar wasa dabal’urarsa ko maɗigo ko nau’rorin zamani na biyan buƙata ba. Wato “Baby ko Boy doll ”
Yin hakan , alama ce dake nuna yana buƙatar aure , don haka wajibi ne ya yi don ya kare kansa daga tafarkin halaka .
Amma ga wanda zai iya mallakar kansa kuma ba ya ƙyamar auren ya zaɓi ya zauna haka ba aure to ba wajibi ne ya yi ba. Musamman idan ya shagala da aiwatar da wasu abubuwa na taimakon addini kamar ianyatrwa da makamantansu.
Shehin Malami Abu Gudda ya wallafa littafi guda na manyan Malamai da suka fifita ilmi akan aure. Ya kawo malamai kusan talatin da y’an kai, maza da mata, mashahurai, sanannu, gogaggu masu tsoron Allah, waliyan Allah, waɗanda har suka koma ga Allah ba wanda ya yi aure a cikinsu.
Ba don suna ƙyama , ko suna gudun auren ba, sai don rayuwarsu ta shagaltu da wani aiki wanda ba su gama shi ba suka koma ga Allah.
3- Malamai na uku su ne waɗanda suke da ra’ayin cewa shi aure ba wajibi ba ne ba kuma mustshabbi ba kai tsaye.
Suna ganin shi hukuncinsa yana sassaɓawa ne da saɓanin mutane suka sassaɓa.
Don haka ba za a iya cewa wajibi ne ga kowa ba. Kuma ba za a ce mustahhabi akan kowa ba. Ya danganta da mai yin auren.
Don haka ba wajibi ne akan kowa ba. Kuma ba mustahabbi ne akan kowa ba Ya danganta da mai yin aure.
Akwai mutumin da aure yake wajibi akansa, shi ne mai ikon da ba zai iya kamewa ba.
Akwai wanda aure yake mustahabbi a kansa , shi ne mai ikon da zai iya kamewa.
Akwai wanda aure yake haramun a kansa, shi ne wanda aure zai kai shi ga sarayar da haƙkin Allah ko zai kai shi ga zaluntar iyalinsa ta hanyar hana su haƙkoƙinsu koda kuwa yana da iko.
Akwai wanda aure yake makaruhi akansa, shi ne wanda aure zai kai shi aikata abubuwan ƙyama da zubar da ƙima. Ko ya kaishi da shagaltuwa ga barin wasu ayyuka muhimmai da suke taimakawa al’umma kamar karantarwa kuma shi ga shi ba mai ƙarfin sha’awa ba.
Akwai wanda aure yake halal a gurinsa shi ne wanda aure ba zai canja masa wani yanayi ba.
Wannan shi ne abin da mazhabarmu ta Malikiyya da wani ɓangare na malaman Shafi’iyya da na Hanabila suka tafi akai. Suka ce na farko aure ya kan zama wajibi akan wani mutum. To waye wannan wanda wajibi ne ya yi aure? Suka ce mutumin da yake da sha’awa mai qarfi kuma yana da buqata zuwa ga saduwa da mace. Wanda idan bai yi aure ba, ko idan ba ta yi aure ba akwai tsoron suna iya faɗawa zina. To wannan tsoron za a faɗa zina ɗin, ko ganin alamun haka, to wajibi ne ya yi aure domin ya kare kansa; itama mace wajibi ne ta yi aure domin ta kare mutuncin ta.
Abinda wajibi ba ya cika sai da shi to ya zama wajibi. Ma’ana tsare kai wajibi ne, to amma sai ya zama hakan nan ba zai yiwu ba sai an yi aure, ka ga aure ya zama wajibi kenan domin a tsare mutuncin kai. Sai malaman suka ce matar da ta samu kanta a irin wannan yanayi, da namijin da ya samu kansa a irin wannan yanayi, wanda in bai yi aure ba zai iya faxawa halaka, to ko da ya tsare kansa daga halaka ɗin, wajibi ne yayi aure. Wannan shine kaso na farko da suka ce maganar aure.
Abubuwa dai da ake awo da su , su ne yanayin kula da haƙƙin Allah da haƙƙin iyali da kuma buƙatar shi kansa mai auren. Sawa’un namiji ne ko mace. Ɗaya zai aura ko fiye da ɗaya.
Abin da ake cewa wajibi shi ne abin da ya zama dole ta yadda idan mutum bai aikata ba ya yi laifi.
Mustahabbi kuwa shi ne abin da idan mutum ya aikata zai samu lada. Amma idan bai aikata bai yi laifi ba.
Shi kuwa haram shi ne abin da idan ka aikata shi kana da zunubi. Amma idan baka aikata ba zaka samu lada.
Mai biye masa shi ne makaruhi wanda cikin aikata shi babu laifi. Amma akwai lada cikin barinsa
Na ƙarshe shi ne Mubahi. Wato abin da yinsa da barinsa duk ɗaya ne.
Babu laifi ma’aurata ko wani daga cikinsu ya sarayar da wani haƙƙi nasa, don a samu daidaito da kyautata zamantakewa. Matsawar dai hakan ba zai kai ga shiga halin ƙaƙa na kanyi ba.
Kamar yadda ba a yarda da sarayar da wani hakƙi na Allah ba.
Malamai sun yi saɓani dangane da waɗannan hukunce hukunce na aure guda biyar.
Shin sun taƙaita akan namiji ne kawai ko kuwa hukuncin ya haɗa har da mata ?
Wasu malaman sun tafi akan cewa wannan hukuncin bai shafi mace ba. Su a gurinsu mata dole ne su yi aure. Ba ya halatta ga wata mace ta zauna babu aure kodan kare kanta daga zargi.
Amma wasu malaman suna da ra’ayin cewa , kamar yadda hukuncin auran maza ya kasu kashi biyar.
To su ma mata hukuncin aurensu kashi biyar ne kamar na maza.
Masu wannan ra’ayin suna kafa hujja da hadisin Abu Sa’idul Khudri cewa: Wani mutum ya kawo ƙarar ƴarsa wajen Manzon Allah (SAW) Ya ce ya rasulallah wannan ‘yar tawa ta ƙi ta yi aure.
Sai Manzon Allah ya ce da yarinyar, ke ki je ki yiwa baban ki biyayya ki yi aure.
Sai yarinyar ta ce a’a ya rasulallah ba zan yi ba har sai ka bani labarin haƙƙin da miji yake da shi a kan matarsa. Idan na ji zan iya sai na yi.
Ta sake maimaitawa Annabi. Shi ma ya sake maimaita mata. Da ta sake maimaitawa.
Sai ya ce, to hakkin da miji yake da shi akan matarsa shi ne, da za a ce miji yana da gulando, ko maruru, ko kaluluwa, a ce ciwon ya fashe yana fitar da mugunya, ko yana zubar da jini. Ko kuma a ce hancinsa ya fashe yana zubar da mugunya ko yana zubar da jini, mace ta zo ta sa harshenta tana lashe wannan jinin, ko wannan mugunya da ke fita daga wannan ciwo ko gyambo, ko gulando, ko maruru ko, kaluluwa, to ba za ta iya biyan haƙƙin mijinta ba.
Sai wannan yarinyar ta ce “wai wai wai, na rantse da Allah da ya aiko ka, bazan yi aure ba har abada. Ba zan iya wannan ba.”
Sai Manzon Allah (SAW) ya ce ” kada ku aurar da su sai da izinin waliyan su “.
Abin lura anan wannan yarinyar Manzon Allah ya ƙyale ta da ta ji cewa ita ba za ta iya sauke haƙkin miji ba tunda dai ba za ta yi zina ba. Saboda haka aka ƙyale ta da ta ce ba zata yi aure ba.
Da wannan wannan hadisin malamai suke ganin cewa akwai uzurin ƙin yin aure ga wacce ba za ta iya kula da auren ba, sannan ba za ta iya biyan haƙƙin mijin ba matuƙar ba za ta yi zina ko ta jawo wa babanta zagi ba.
Idan za ta jawowa babanta zagi ko abin faɗe kuwa to dole ta yi aure tunda za a iya cewa ya bar ‘yarsa ta gandame a gida.
A al’adance ma mata basa jin daɗin rayuwar idan suka girma suka gansamewa a gaban iyayensu, musamman su da ba zasu fita shagunan waje ko soron gida kamar namiji ba.
A irin wannan yanayi ta hanyar aure ne kawai za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali.
Don haka zai fiye mata ta yi aure koda kuwa ba zata ji daɗin auren sosai ba. Fiye da zama a yananin da zata damu kanta ta damu wani.
Zaɓar ƙaramar matsala akan babba yana daga ginsheƙai na koyarwar musulunci.
Allah masani.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button