Hotunan auren ɗan gwamnan Jihar Jigawa da zuƙeƙiyar budurwarsa da suka hadu a Snapchat
Dan gwamna Mohammed Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya angwance da budurwar sa, Affiya Sadiq Umar a ranar 11 ga watan Satumban 2021
An samu rahotanni akan yadda ya hadu da tsaleliyar budurwar a kafar sada zumuntar zamani ta Snapchat
Kamar yadda mai hoton su ya bayyana a shafin sa na Instagram ya ce soyayyar ta fara ne bayan Abdul ya yi tsokaci akan hoton Affiya
Jihar Jigawa.
Hoto :atilary studio
Hoto :atilary studio
– Dan gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya zama angon zankadediyar budurwar sa a ranar 11 ga watan Satumba bayan haduwar su a wata kafar sada zumuntar zamani ta Snapchat.
Kamar yadda Legit ta ruwaito, mai hoton bikin su, Atilary ne ya wallafa hakan a shafin sa na Instagram a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, inda ya bayyana cewa soyayyar ta su ta fara ne a kafar sada zumunta bayan Abdul ya yi tsokaci akan hoton ta.
Waye ya ce soyayyar kafar sada zumunta karya ce?
Kamar yadda mai hoton ya wallafa:
“Waye ya ce soyayyar kafar sada zumuntar zamani karya ce? Soyayyar ta fara ne tun bayan Abdul ya ga hoton ta a Snapchat ya rude ya yi mata tsokaci da “cutie” ma’ana kyakkyawa. Kuma a ranar ya ce ya hadu da matar sa kuma ga shi ya tabbata.”
LIB ta ruwaito yadda mai hoton ya wallafa kyawawan hotunan su masu daukar hankalin mai kallo.