Gaskiyar Labari Hadiza Gabon Nason Zama Matar Sheikh Pantami – Daga Hadiza Gabon


A yan kwanakin nan wani labari yayi ta yawo a kafar sada zumunta cewa Hadiza Gabon ta sha alwashin sai ta zamo matar sheikh Isah ali Pantami wanda wannan labarin ya dauki yan kallo sosai a kafar sada zumunta musamman ta facebook.
Ga labarin da yayi yawo a kafar sada zumunta na facebook daga wani shafin mai suna hausa daily times.
“Fittaciyar jarumar masana’antar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon, ta bayyana yadda ta kamu da matsanaicin soyayyar Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.
Hadiza Gabon wacce ake wa laƙabi da uwar marayun Kannywood, na daga cikin jarumar masana’antar mata attajirai, ta kuma ce ba kuɗin Malamin ne ya ja hankalinta ba, domin a wadace take. Ta shaida cewa a shirye take a kowani lokaci ta daina yin fim idan har Sheikh Pantami zai aure ta, kamar yadda Neptune Prime ta ruwaito.
A cikin wani gajeren bidiyon da ta ɗora a shafinta kuma yake yawo a shafukan Instagram da Facebook, ta yi alƙawarin zama mace tagari, mai addini da bin ƙa’odojin mijinta har da zama matar kulle idan Pantami ya buƙaci hakan.
Ta ce bata da wani babban buri a yanzu da ya wuce ta yi aure ta haifi ƴaƴa kuma Sheikh Pantami ne burinta kuma shi take ta yin mafarkin ta zama matarsa a ƴan kwanakin nan.”
To sai dai majiyarmu hausaloaded tayi shiru tana binciken shahin labarin wannan maganar wanda Allah a yau mun zamu tabbaci daga ita jarumar.
Wani mabiyin jarumar a kafar Instagram bayan ta wallafa wani gajeren bidiyo daga tik tok tana rera wakar wani mawakin turanci sai yayi mata tambaya kamar haka.
“@mujee A yanzu nan na karanta wani labarin jita jita cewa babban burin ki a rayuwa ki auri prof isah ali pantami”
“@adizatou Ba gaskiya bane“.
Allah yabata kuma Allah yabasu zaman lfy