Labarai

El-Rufa’i ya haramta sana’ar Achaba don yaki da ƴan bindiga a Kaduna

El-Rufa’i ya haramta sana’ar Achaba don yaki da ƴan bindiga a KadunaGwamnatin jihar Kaduna ta sanar da haramta sana’ar haya da babura da aka fi sani da Achaba ko Okada a jihar domin dakile matsalar tsaro a jihar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Samuel Aruwan, inda sanarwar ta ce masu Keke Napep za su rika aiki daga karfe 6 na safe zuwa 7 na dare.
Dcl sun ruwaito cewa sanarwar ta kuma ce, gwamnatin jihar ta sanya dokar cewa duk masu motocin haya su yi musu fenti launin dorowa da baki nan da kwanaki 30.
Samuel Aruwan ya ce an kuma hana sana’ar bumburutu wato sayar da fetur a cikin jarkoki da galaluwa a kananan hukumomin Kajuru, Chikun, Kachia, Kagarko Birnin Gwari da Giwa.
Sanarwar ta ce ana nan ana shirye-shiryen katse layukan sadarwa a wasu sassan jihar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA