Dokar hana yin fim kan aikata ta’asa: Afakallah ya biyo layin hauka, inji Falalu Ɗorayi
FITACCEN jarumi, furodusa kuma darakta Falalu A. Ɗorayi, ya yi fatali da dokar nan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ƙaƙaba wa Kannywood wadda ta haramta shirya fim kan ayyukan ta’asa irin su kidinafin, shaye-shaye da ƙwacen waya.
Idan kun tuna, shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya bayyana wa mujallar Fim a ranar Talata da ta gabata cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin kare mutunci da al’adar mutanen Kano.”
Ɗorayi, wanda ya na ɗaya daga cikin masu shirya fim da ake ganin wannan dokar za ta shafa, ya faɗa wa mujallar Fim cewa kwata-kwata Afakallahu bai yi aiki da hankali ba kafin ya yi wannan dokar.
“Mutumin nan ya na tafiya ne kawai ya na ta hauma-hauma,” inji shi.
A hirar musamman da ya yi da mujallar Fim kan sabuwar dokar ta Afakallahu, daraktan ya ce, “Abin tambaya a nan shi ne da me ya dogara da zai ɗauki wannan mataki duba da cewar komai in za a yi ana fara tattara masu ruwa da tsaki kan lamarin ne a yi magana da su cewa ga wani abu da gwamnati za ta yi a matsayin ku na wanda mu ke tare da ku na cewa finafinai da ake ko a juya akalar su a gyara a ɗan daina saboda abin ya fara ta’azzara? Amma kai-tsaye ka ce za ka yanke hukunci a matsayin ka na gwamnati, ya zama kamar mulkin soja kenan ko?
“Ba wata doka da ta ce ba za a nuna fim na shaye-shaye ba, ba za a haska fim na abin nan ba.
“Ai har yanzu ana yin fim ɗin Amurka, kuma har gobe su na yin fim a kan masu tada ƙayar baya. Fim ɗin 11 ga Satumba da aka yi na kai masu hari a kan Pentagon da waye-waye har gobe su na fim a kai da yadda su ka tsara abin da yadda su ka je su ka kai masu harin, har gobe ana yi.
“Kuma har gobe su na fim ɗin ‘yan tada ƙayar baya da su ke son kai wa Amurka hari. To amma abin da ake nunawa, ƙarshen waɗannan mutanen bai yi kyau ba.”


Ɗorayu ya ce, “Yau na yi tunanin abin da zai faɗa kenan a kan cewa duk fim ɗin da za a yi a kan ɓatagari idan a ƙarshen fim ɗin ba a nuna wani abu da ya same shi ba a kan abubuwan da ya ke aikatawa, to ba za a karɓi wannan fim ɗin ba. Wannan layi kenan na hankali, ba wai na hauka ba.
“Akwai wani abu da mutane ba su gane ba: gwamnati ta na ɗaukar mutane ta na ba su muƙamai saboda kawai mutum ne ya ke kallon ya je wani wuri sai ya manta da dokokin da su ka kafa shi, sai ya fara aiki da hankalin sa kawai.
“Kuma mafi yawan hankalin da su ke amfani da shi ba masu hankali ba ne, saboda ba zai yiwu mutanen da su ka doshi wajen miliyan sittin da su ke fim kama daga Kaduna, Kano, Abuja da sauran jihohin Nijeriya, ka zauna kawai a cikin ɗaki a Kano wai ka ce kai ka kafa doka. In ka yi wa ‘yan Kano wannan tarnaƙin, sauran ‘yan garuruwa ya za a yi da su? Na ɗauka ana bin abu cikin masalaha ne da hankali.”
Daraktan ya ce kamata ya yi shugaban hukumar ya zauna da masu ruwa da tsaki da ke cikin wannan masana’antar ya fara bayyana masu ƙudirin sa na cewa ana so a dakatar da wannan ɗabi’a ta nuna shaye-shaye da kidinafin da sauran su a finafinai, a ɓullo wa al’amarin tare, ba wai a yanke hukunci kai-tsaye ba.
Ɗorayi ya ce abin da ya dace Afakallah ya yi shi ne ya zauna da su ya gaya masu cewa, “Ana yin finafinai na ‘yan tada ƙayar baya kwanan nan, waɗanda su ke yin mugun abu, ana ta nuna su, abin nan ba ya yi wa mutane daɗi, mutane na ta magana, to mu na da shawara a kan ku – ku masu shirya finafinai – ya kamata ku rage yin finafinan, ku koma na kaza da kaza.”
Ɗorayi ya ce, “Wannan shi ne ya nuna hankali, amma ba wai kawai ka ɗebi ɗan wake a cikin ɗaki kawai ka zauna ka yanke hukunci ka ce wai doka ce ba! Wannan ya na buƙatar a duba kan su gaskiya.”
Kuma ya ce Afakallah ba ya bin doka shi kan sa. Ya ce, “Abin da ya sa Afakallah ba ya ban mamaki shi ne gaba ɗaya duk wani abu da ya gina, doka ya ƙetare tun da daɗewa, to shi ya sa in ya yi wani abin gaba ɗaya ba ya ban mamaki. Dalili kawai yanayi ne; misali, inda ka san mahaukaci ne ka tuna masa cewa ba ya duka sai ya ce, ‘Au, ka ma tuna min!’ Abin da na ɗauke shi kenan, saboda duk abin da ya ke ba ya bin doka, saboda ni ta faru da ni.
“Haka ya zo ya sa fim ɗi na na ‘Gidan Badamasi’ a gaba lallai sai ya hana an nuna a Arewa24. Na tambaye shi meye dalili, ya kasa kafa hujja.”
A cewar Ɗorayi, dokar hukumar ma ba ta hau kan finafinai masu dogon zango ba.
“Hasali ma dokar ka ma ba ta da hurumi a kan finafinai masu dogon zango da ake nunawa a gidan ralabijin. Ka je ka duba dokar. Haka ya zauna ya na ta fafutika.
“To, tun daga nan na gane cewa mutumin nan ya na tafiya ne kawai ya na ta hauma-hauma.
“Ya kamata gwamnatin ta riƙo shi ta miƙa mishi sanda saboda bai san me ya ke karantawa a cikin dokar sa ba.”
A ƙarshe, Ɗorayi ya bayar da wasu shawarwari, inda ya ce, “A matsayin su na hukuma, su koma su ƙara duba dokar nan, a duba cewa waɗanda mu ke mulka, wato al’umma kenan, mu duba mu ga cewa shin sun san da wannan dokar ma tukuna?
“Ka zauna da ƙungiyoyin su in dai da man ba don saboda ya raina ƙungiyoyin ba saboda ya saka sauran ƙungiyoyin a aljihu, mu irin mu ne dai ‘yan taratsi har yanzu mun ƙi sakuwa a aljihu, amma dai duk wata ƙungiya a Kano, ni yanzu ba na kallon ta a matsayin wata ƙungiya da za ta iya taka masa birki ko ƙalubalantar sa. To amma tunda su na yi maka biyayya, ka maida su ‘yan matan ka, ko da yaushe ka ga dama hawan su ka ke yi, abin da ya kamata shi ne ka zauna da su ka fara duba su, su zauna da kai, sai ka ce, ‘Ga dokar da mu ka fito da ita, ku kuma wanda ku ka yi fim masu irin wannan abin ku je ku gyara fim ɗin, idan ba ku nuna wannan mutane su na da ƙarfi ba in kuma kun nuna ma ya yi daidai, abin da mu ke buƙata kenan. Amma idan ku ka nuna ba su da ƙarshe, to ku gyara ƙarshen, za mu ci gaba da mu’amala da ku.’ Wannan ita ce gaskiya da amana.”
Shi dai Falalu A. Ɗorayi, kwanan nan wani kamfani ya karrama shi kan wani fim da ya shirya a kan kidinafin da harin ‘yan bindiga kan ƙauyuka mai suna ‘Ishara’.
A fim ɗin, an nuna yadda mutane su ke zama sakaka ba tare da su na ɗaukar matakin daƙile harin ɓatagari ba ta hanyar yin kwamitin unguwa da fito da halayyar asali ta Fulani da dalilan da ya sanya ake masu wani kallo.
Karshen zantawa Mujallar Fim da Falalu daroyi kenan da munka dauko muku daga mujallar