Kannywood

Dalilin Da Yasa Na Zama Mawakiya – Hauwa Yar Fulanin Gombe

Advertisment

Dalilin Da Yasa Na Zama Mawakiya – Hauwa Yar Fulanin Gombe
Hauwa Yar Fulanin Gombe

Shahararriyar mawakiyar nan mai suna Hauwa Ƴar Fulanin Gombe, wacce ta shahara a fagen rera wakokin Hausa dana Fulani a Nigeria, ta bayyana wa duniya dalilin da yasa ta fara harkar waka.
Jarumar ta bayyana haka ne cikin wata fira da tayi da wani shafin sadarwa na Internet mai suna W TV, ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance.
GABATARWA
“Ni dai suna na Hauwa Ƴar Fulanin Gombe” an haife ni ne a garin Gombe, nayi primary school da secondary school a garin Gombe, naso naci gaba, amma Allah bai nufa ba, kila ko sai nan gaba.
DALILIN DA YASA NA FARA WAƘA
Shine lokacin ina secondary school, to ban gama ba sai nayi Aure, sai bayan da aure na ya mutu na dawo gida, sai na koma makaranta na ka rasa SSCE bayan na gama na koma gida ina zaune, na dan nemi makarantu daban daban, amma Allah bai yi ba, sai na fara sana’ar zannuwa irin na mata, to da yake kasan mutane bashi yayi yawa abun akwai wahala sai na daina.
Babban dalilin da yasa na fara waƙa shine lokacin da ƙanina ya zama Soja, sai naji ina son ayi masa waƙa, kuma ina son mace ce tayi masa waƙa kamar ni, sabo da tun farko na taso ina son waƙa, to sai Allah ya kaddara na rasa wacce za tayi masa sabo da a lokacin gaskiya babu mawaƙa mata
Sai nayi ma wani mawaƙi magana nace ina so ayi mun waƙa ne, amma mace nake so tayi mun waƙar sai yace mun gaskiya ba’a samu macen da zata yi ba sabo da a lokacin babu mawaƙa mata a Gombe, sai yace mun to ke kiyi mana, sai nace masa ai bazan iya ba, sai yace zaki iya, sai yace ai zai rubuta mun, daya rubuta mun sai ya bani yace kije kibi, sai naje gida bayan kwana biyu muka je Studio, da yake lokacin cikin Gombe Studio ɗaya ne, sai munje ace sai gobe, akwai ranar ma da sai da na shiga cikin wurin rerawa aka ce na fito sabo da zan wahalar tunda yanzu zan fara
Sai na fito ya shiga ya gama ya fito, yana fitowa na shiga tunda na fara ban tsaya ba sai da na gama, sai kowa ya cika da mamaki, Studiyon sai suka fara jin daɗi, suna cewa kaji murya kamar Fantimoti gaskiya kinyi kokari kinyi kokari, daga nan sai mai Studiyon yace mun zasu karɓi number na idan an tashi amshi zasu kira ni wannan shine dalilin da yasa ba fara waƙa.
KALUBALE
Dama kamar yadda na faɗa tun farko na tashi ina son waƙa sosai, amma ban taɓa tunanin zanyi waƙa ba a rayuwa ta ba, kuma banyi zaton gidan mu zasu barni na fara waƙa ba, amma da yake Allah ya rubuta kuma akwai abinci na a ciki, dana fara na samu wahalhalu sosai a ciki, domin na ɓata da mutanen gidan mu karshe suka zo suka fahimce ni aka bani dokoki waɗanda nake tafiya akan su.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button