Kannywood

Dalilin Da Yasa Ake Kira Na Mai Sana’a – Musa Mai Sana’a

Dalilin Da Yasa Ake Kira Na Mai Sana'a - Musa Mai Sana'aTsawon lokaci ba a ganin fitaccen jarumin Barkwanci Musa Maisana’a ba a cikin wani sabon Fim, wanda hakan ya sa mutane su ke tambayar ko dai Maisana’a ya daina yin fim ne?
To sai dai a tattaunawar sa da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, ya tabbatar da cewar, har yanzu yana cikin harkar fim bai daina yin ta ba.
Musa Maisana’a ya ce “Ai ni harkar fim na dauke ta sana’a ce, don haka ban shirya barin ta ba a yanzu, sai dai in kai ne a yanzu za ka koreni, don haka ina cikin ta kuma babu wani lokaci da na ke tunanin zan bar ta.” Inji Shi.
To ko me ya sa ba a ganin ka?
“Abu ne da ya zo da sauyi a ita masana’antar, wadda harkar fim din ta sauya Salo, domin ka san a baya fina-finan kasuwa a ke yi, wanda za mu yi fim mu kai kasuwa”
“To yanzu kuma sai ya zama harkar ta sauya, sai dai a yi fim na gidan TV ko kuma a dora a YouTube, to da yake ina da harkokin kasuwanci da na ke yi, sai na fi bada karfi a can, Amma dai har yanzu ina harkar fim don yanzu ma a wajen aikin fim ka zo ka same ni, don haka ina yin fim kuma ina harkar kasuwancin Motoci da sauran abubuwa, ba Wai kawai harkar fim na ke yi ba, daman tun tasowa ta ina kasanci Kala Kala, shi ya sa ma aka saka mun sunan Musa Maisana’a, ” a cewar shi.
Daga karshe ya yi godiya ga masoyan sa da su ke kulawa da shi, wanda har su ke ci jiyar sa da suka ga ba ya fitowa a fim sosai.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button