Kannywood

Bello Muhd Bello Ya Fadi Wani Babban Alkhairi Da Abdul Amart Yayiwa Iyalinsa

Bello Muhd Bello Ya Fadi Wani Babban Alkhairi Da Abdul Amart Yayiwa Iyalinsa
Abdul Amart Mai Kwashewa

A kwana kin bayya bello Muhammad bello wanda ake kira da General BMB ya samu kyautar babban motar a wajen babban darakta Abdul amart mai kwashewa wanda yayi kalamai masu ban mamaki da hikima akan irin yadda yayiwa iyalinsa da rayuwarsa kyaututuka da dama bayan wannan mota.
Jarumi Bello Muhammad Bello yayi kalamai na godiya tare da bayyana wasu sirruku da mai kwashewa yayiwa Bello Muhammad Bello kamar yadda tya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Bello Muhd Bello Ya Fadi Wani Babban Alkhairi Da Abdul Amart Yayiwa Iyalinsa
Motar da Abdul Amart Mai kwashewa Ya Baiwa BEllo Muhammad Bello

Sunanshi ABDUL AMART MAIKWASHEWA @abdulamart_mai_kwashewa
Yana da muhimmanci a wajena mara misaltuwa saboda:
1- ZAKI ne shi mai fita farauta, sai yayi zagaye, ya farauto, ya rike sannan yacewa duk kuzo muci tare.
2- Yana gasa kifi ya baka, amma yafiso ya ja ka ya koya maka yadda ake kamun kifin.
3- Yana daura ka a channel din da yakamata kabi ka samu arziki kuma ya shige maka gaba har sai ka samu da ikon Allah, kuma baya neman kaso daga gare ka.
4- Idan zai baka kyauta ko gida ko mota duk tsadarsu baya dauka a waya kuma baya so a dauka a waya balle ma a nunawa duniya.
5- Wallahi bazan iya lissafa iya kyaututtukan da yamin ba daga kan Kudade, motoci, wayoyi, kayan abinci da makamantansu ba.
6- Wallahi ko yau ka ganni da sabuwar mota idan har ba’a daye leather na seat din ba ko shakka karkayi, daga wajenshi Allah ya fitomin da Ita don a hada ta da ‘yanuwanta.Bello Muhd Bello Ya Fadi Wani Babban Alkhairi Da Abdul Amart Yayiwa Iyalinsa
7- Shine ya chajawa Twins dina Makaranta.
8- Yana da jajircewa wajen Ibada kuma hadimi ne, masoyi ne na ANNABI MUHAMMDU SAW.
9- Babu wanda yake tare da shi da zaiyi kuka da shi, duk wanda yake tare da shi, kaji ya tsoki Abdul Amart to cikin biyu ko mutum munafuki ne ko mai hassada ne.
10- Baya gaba, baya riko, baya hassada sai dai ayi gaba dashi, a rike shi a zuciya ko ayi hassada da shi.
11- Ko a shafinshi na yada zumunci ba shi da wasu kalamai da ya wuce “ALLAH KA IYAR MANA, ALLAH KA SHIGE MANA GABA.
12- Iya zama na da shi ban taba jin yana gulmar wani ko wata ba kuma ban taba ganin ya bada fuska an kawo gulmar wani ko wata ba.
#maimuhimmancichallenge”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button