Addini

Abinda ya hadani da lauyoyi na-Sheikh Abduljabbar Kabara

Advertisment

Abinda ya hadani da lauyoyi na-Sheikh Abduljabbar Kabara
Abinda ya hadani da lauyoyi na-Sheikh Abduljabbar Kabara
Malamin Addinin musuluncin nan a nan Kano Sheikh Abduljabbar Kabara ya bayyana abinda ya hadashi da lauyoyinsa har suka juya masa baya.
Malam Kabara ya ce lauyoyinsa sun bukaci ya basu N 1,500,000 domin su shirya taron manen labarai.KANO FOCUS ta ruwaito malamin ya bayyana hakan ne lokacin da yake yiwa kotu bayani, a wani bagare na ci gaba da shari’ar da ake yi masa.Ya ce sun nemi kudinne da zummar su yi taron manema labarai sununa yadda aka zalinceshi ko jama’a sa tausaya masa.
Ya kara da cewa kwanaki biyu kafin a yi zaman kotun baya lauyoyinsa sun samenshi a gidan kurkuku, suka ce masa za a koma kotu za kuma a ci gaba tuhumarsa.
“Sun sameni a gidan yari na Kurmawa, inda nake tsare, suka ce min dukkan tuhumar da ake yimin gadar zarece kawai.
“Sunce idan na amince da tuhumar to ba shakka na fada cikin tarkon da aka danamin.

“Suka kuma gayan tuni aka yankemin hukunci jira ake kawai na amsa a zartar da shi.” A cewarsa.
Na zama kurma
Sheikh Abduljabbar Kabara ya kara da cewa lauyoyin sun bukaci da ya kame bakinsa da zarar anje kotun kada ya ce uffan.
Ya ce sai dai ya tambayesu mai zai biyo baya idan ya kulle bakinsa ya ce ba zai yi Magana ba?
Inda ya ce sun gayamasa kar ya damu za su kula da al’amarin, shi dai kada ya yi Magana.
Haka kuma ya ce sun nemi ya basu N500,000 domin su shirya taron yan jaridar.
“Bayan sun gama wancan bayaninne kuma suka bukaci na basu dubu dari biyar su yi taron ‘yan jarida.

“Hakan ta sanya na basu N300,000, na kuma zo kotu na kame bakina kamar kurma”.
“Bayan na kame bakina ne kuma alkali ya ce a yi min gwajin kwakwalwa da na kunne, amma lauyoyin nan suka kasa cewa komai”, ya kara da cewa.
Wani jami’in gwamnati zai taimakeni
Abduljabbar Kabara ya ci gaba da gayawa kotu cewa, lauyoyin nasa sun hada shi da wani babba a gwamnati don ya taimaka masa.
Ko da dai ya ce ba zai fadi sunansa ba, amma ya yi masa wasu bayanai.

Dole na yarda inda ciwon hauka
Malamin ya ce mutumin da aka hada shi da shi ya gaya masa idan aka tabbatar da shi mahaukaci ne to rayuwarsa za ta tagayyara.
Sai dai ya gaya masa zai kuma shaki isakar ‘yanci, amma zai ci gaba da rayuwarsa a matsayin mahaukaci.
Don haka ya ce sun nemi ya basu milyan daya, don su kira taron manema labarai a karo na biyu su magance duk wani abu da zai batamasa suna.
“Sun nemi na basu N1,000,000 su yi taron manema labarai, don su karemin martabata da sunana.
“Amma sai sukace dole idan za a yi haka sai na yarda inada tabin kwakwalwa, sannan za su taimakamin a sakeni.
Za a kwace min mata
Haka zalika malamin ya ce lauyoyin sun yi yunkurin kwace masa mata.
A cewarsa bayan da aka bukaci a yi masa gwajin kwakwalwa lauyoyin sun yi kokarin kulla alaka da matarsa.
Ya ce al’amarin bai yi masa dadi ba, inda ya ce hakan cin zarafi ne.

Zarge-zargen ba gaskiya bane
Sai dai lauyoyin na sa sun musunta dukkanin zarigin da malamin ya yi musu.
Barrister Rabi’u Shu’aibu Abdullahi ne ya musanta zargi a wani bagare na mayar da martani ga kalaman na Sheikh Abduljabbar.
Ya ce idan Abduljabbar yana gani an yi masa ba dai-dai ba to akwai inda aka tsara ya kai karar lauyoyin.
Ya ce idan ya kai kara a nan ne lauya zai kare kansa kan duk wani zargi da aka yi masa,
Ko ya shigar da kara ko mu bi hakkin mu
Haka zalika Barrister Abdullahi ya ce sun baiwa malamin makwanni biyu ya shigar da karar neman hakkinsa kan zargin da yake yi musu.
Ya ce hukumar da aka tanada don kai karar lauya ba a boye mata dukkanin bayanai.
A don hakan nema ya ce sun bashi makwanni biyu ya kai karar ko kuma su su nemi nasu hakkin.
 

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button