Abin Da Ya Sa Ba Zan Fito A Fina-finan Kudu Ba- cewar Umma Shehu
Shehu, ta bayyana cewar, ita fa ba za ta fito a cikin fina-finan kudu
ba, saboda ya saba wa addinin ta
Jarumar ta ce “Ni Musulma ce, kuma addini na bai yarda da wasu
abubuwa da a ke yi a cikin fina-finan kudu ba, kamar
rungume-rungume da wasu abubuwa da suka saba wa addini na”
inji ta”Ni mace ce gaba zan duba, idan na duba abin ba zai taba ni ba sai
na yi, ba wani abu ba ne
Amma fa abu ne na addini, yanzu komai
mutane idan an tashi sai su ce addini” a cewar ta.Kazalika Umma Shehu ta ce, “Wallahi duk abin da namiji ya yi ado
ne, ba kamar mace ba
Mace duk abin da ta yi yana nan a ajiye,
wata rana za a fada wa ya’yan ki, don haka dole ne mu mata mu
rinka kiyaye yadda za mu tafiyar da rayuwar mu, don gudun bar wa
yayan mu abin fada