Abin ƙyama mafi muni: An kama ɗa da ya yiwa mahaifiyarsa ciki har sau uku
Ana kyautata zaton lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.
Bisa labarin, matar yanzu haka, ta riga data haifa wa ɗanta yara har uku.
Mahaifiyar mai suna Fati Sime, ta koma ƙauyen daga Jamhuriyar Benin tare da ɗanta ne mai suna Fati.
Kamar yadda Jaridar Mikiya na ruwaito.A cewar mazauna yankin, Adamu Sabi Sime da wani ɗan Fati an kuma ce suna kwanciya da mahaifiyar ne duk wanda suka buƙaci hakan.
Kuma a halin yanzu an ce shi Fati ya yi ɓaan dabo, sakamakon kama dan uwansa ƴan jami’an tsaron sibil difens na jihar Kwara suka yi, wato (NSCDC).
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga majiyarmu ta samun wannan bayanin, a Ilorin ranar Lahadi.


Kakakin Hukumar NSCDC na Jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi, ya bayyana mana cewa tuni an miƙa mahaifiyar da ƴaƴanta guda biyu ga Hukumar Shige da Fice ta Najeriya don ci gaba da bincike saboda an yi imanin ba su da takaddun da suka dace don ci gaba da zama a Najeriya.
Ga bayanin sa:
“Haka ne, lamarin gaskiya ne. Mallam Bandede, Hakimin Gundumar Mosne a Kaiama ne ya kawo mana rahoton.
“Lokacin da jami’an mu na Kaiama suka isa wurin, mun gano cewa mahaifiyar (Fati) tana da yara uku ga Adamu Sabi, ɗan ta na haihuwa.
“Binciken da aka yi ya nuna cewa ƙanin wanda ake zargi, wanda shi ma aka tabbatar yana kwanciya da mahaifiyar, yanzu ya arce,” in ji Babawale.
Wasu daga cikin mazauna garin Kaiama, sun yi kira ga hukumar shige da fice da su ci gaba da yin ƙwaƙƙwaran bincike na baƙi da ke yin hijira zuwa cikin kasar nan.