Labarai

Sarauniyar kyau ‘yar kasar Rasha ta Musulunta ta auri Sarkin Malaysia

Advertisment

Oksana Voevodina tare da mijinta

Sarauniyar kyau ta birnin Moscow dake kasar Rasha yanzu ta zama Sarauniyar kasar Malaysia bayan ta auri Sarkin kasar jim kadan da komawar ta addinin Musulunci.
Sarauniyar kyan ta Moscow, Oksana Voevodina, mai shekaru 28 a yanzu ta auri Sarki Muhammad na V, mai shekaru 52, inda ya hau karagar mulkin a shekarar 2006.
Oksana Voevodina ta Musulunta a shekarar 2018, ta karbi Musulunci kafin ta auri Sarki Muhammad, kuma har yanzu ba a tabbatar da addinin da take bi ba a baya.

Oksana Voevodina ta Musulunta a watan Afrilun shekarar 2018, anyi aure naa alfarma tsakaninta da Sarkin Malaysia. Anyi amfani da abinci da abin sha wadanda shari’ar Musulunci ta amince da su.
Duk da dai cewa addinin Musulunci shine addini mafi rinjaye a kasar Malaysia, amma kasar ta bawa sauran addinai gabatar da ibadun su ba tare da matsala ba.
Haka kuma kundin tsarin mulkin kasar Malaysia na kallon Sarkin kasar a matsayin shugaban kasar Musulmai.

Kamar yadda jaridar Mirror ta kasar Birtaniya ta wallafa, matar Sarkin ta kammala jami’a a daya daga cikin manyan jami’o’i kasar Rasha, an nada ta sarauniyar kyau a shekarar 2015, tayi aiki a kasar Thailand da kuma kasar China.

Oksana Voevodina Tare da Danta

Ta ce ba taa san cewa tana da kyau ba, har sai da ta shiga jami’a.

Nafi kowa tsawo a ajin mu, kuma nafi kowa rashin kiba, a lokacin duka bana jin dadin yanayin yadda jikina yake, amma bayan shawara dana samu daga makaranta, na samu kwarin guiwa sosai.

Yayin da shi kuma Sarki Muhammad na V, ya kammala jami’ar Oxford, sannan kuma ya yi karatu a kwalejin kasuwanci dake birnin Landan.
Ya auri wata ‘yar kasar Malaysia da farko, amma sun rabu daga baya kafin ya auri Oksana.

Oksana Voevodina Tare da mijinta

Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Source: Islamic Information

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button