Sadiya Haruna Da Umma Shehu Ba Yan Kannywood Bane ~ Alhasan Kwalle
Bayanan hakan na kunshe cikin wani faifayin Bidiyon da shafin kannywood sunka wallafa Jarumi Alhassan Kwalle wanda su ne tsofaffin Jaruman da aka daɗe ana damawa da su ya wallafa a shafin sa.
Ya ce yana so mutane su gane cewar Sadiya Haruna ba Jarumar Kannywood bace, ita ma Umma Shehu tana yin yan abubuwan ta amma dai bata da cikakkun ƙa’idar zama cikakkar Jaruma ba, ma’ana bahaushe zai fahimci muna jaruma ce,ba jaruma ba.
Jarumin Alhassan Kwalle da alama da yana mai mayar da martani ne game da rikita rikitar dake faruwa a yan kwanakin nan a tsaknin hukumar Hisbah da Sadiya Haruna wacce ake alaƙantawa da masanaantar Kannywood.
Alhassan Kwalle yana mai gargaɗar su da cewar ko mai mutun zai yi ya dunga tuna Addinin shi,shafin dimokuradiyya shima yayi hidama a cikin tattatara bayyanan.