Kannywood

Rasuwar dattijuwar Kannywood Umma Ali: ‘Yan fim sun bayyana alhini

MASU harkar finafinan Hausa sun bayyana matuƙar alhini dangane da rasuwar Hajiya Umma Ali, ɗaya daga cikin mata biyu da ake ɗauka a matsayin dattijai a Kannywood.
Hajiya Umma, wadda ita ce mace ta farko da ta jagoranci ƙungiyar furodusoshi mata a tarihin masana’antar, ta rasu ne ɗazu da yamma a Asibitin Premier da ke unguwar Court Road, Kano.
An kai ta asibitin ne da safe sakamakon haki da ta wayi gari da shi.
An yi mata sutura a gidan mijin ta da ke Gyaɗi-Gyaɗi sannan aka rufe ta a maƙabartar unguwar a daren yau.
Hajiya Umma ta rasu ta na da kimanin shekara 63 a duniya.
Ta bar mijin ta mai suna Muhammad Ali, wanda tsohon ma’aikacin hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa ne, wato Kwastom, da ‘ya’yan ta 10, maza shida mata huɗu. Haka kuma ta na da jikoki 11.
Wannan mutuwa ta girgiza ‘yan fim da dama saboda yadda su ka ɗauki Hajiya Umma tamkar uwa.
Mujallar Fim ta ji ta bakin babbar aminiyar ta, wato babbar furodusa Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, wadda ta bayyana kaɗuwar ta matuƙa dangane da wannan rasuwa.
Hajiya Balaraba dai ita ce ta karɓi shugabancin ƙungiyar furodusoshi mata daga wajen marigayiyar.
Ta bayyana wasu daga cikin kyawawan halayen Hajiya Umma a tsawon shekarun su ka yi a matsayin aminai.
Ta ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Masana’ntar shirya finafinan Hausa mun yi rashi saboda Hajiya Umma furodusa ce ta farko, don ta riga ni ma yin fim. Kusan ita ce ta biyu a mata furodusas.
“Mun ji daɗin rayuwa da ita saboda ita aminiya ta ce. Babu wanda ya san tsakani na da Hajiya Umma. Kuma mu ne kaɗai mata da mu ke cikin ƙungiyar dattawan Kannywood, sannan ita ce wacce ta fara mana shugabanci a ƙungiyar mu da mu ka kafa ta furodusas mata a ƙungiyar.”
Ta ƙara da cewa, “Marigayiya ta na da halayya mai kyau. Ta na da son mutane kuma ba ta da fushi, kowa nata ne. Ta na da dauriyar a yi abu da ita saboda duk inda aka kirawo mu wani taro tare za mu je.
“A duk wani rikici da ya shafi mata, ni da ita ake kira mu sasanta, har wata rana ta ke cewa, ‘Mu yanzu an maida mu dai kawai in ba rigima ce ta taso ba ba za a kira mu ba’.”
Bugu da ƙari, Hajiya Balaraba, wata fitacciyar marubuciyar littattafai ce, ta ce marigayiyar ta riƙi jarumai da dama har ma da mawaƙa a gidan ta, waɗanda su ka haɗa da Ibrahim Sharukhan da Dauda Kahutu Rarara.
A nasa saƙon ta’aziyyar, shugaban farko na haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu harkar finafinan Kannywood ta Nijeriya (MOPPAN), Alhaji Sani Mu’azu, ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Haj Umma! Allah ya jiƙan ta. Allah ya yi mata rahama. Allah ya bai wa iyalan ta haƙuri da dangana.”
Ya ƙara da cewa, “Kamar Haj Balaraba, Haj Umma na cikin dattawan wannan masana’anta waɗanda aka yi gwagwarmayar baya da su. Ta taimaka daidai gwargwado wajen haɓaka sana’ar.
“Sannan kuma ta saka ‘yar ta a cikin harkar a wani lokaci, da har na zaci ‘yar ta ce za ta zama mace ta farko ‘director’, mai bayar da umarni, a Kannywood.”
A saƙon nasa da ya wallafa a soshiyal midiya, Sani Mu’azu, wanda kuma babban jarumi ne a Kannywood da Nollywood, ya ce, “Ina miƙa ta’aziyya ta ga masana’antar baki ɗaya. Allah ya kyautata ƙarshen mu gaba ɗaya.”
Shi ma fitaccen jarumi Abubakar Hayatu (Baballe) ya yi alhinin wannan rashi da aka yi.
A saƙon ta’aziyya da ya turo wa mujallar Fim, Baballe ya ce, “Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Allah ya jiƙan Hajiya Umma Ali. Allah ya sa Aljanna makomar ta. Halin ta nagari ya bi ta.
“Tabbas, an yi rashin mace mai son mutane. Hajiya Umma Ali mace ce mai son taimako. In ka je gidan ta ba za ka rarrabe su waye ‘ya’yan ta ba. Ta riƙe mutane da yawa a gidan ta. Ta aurar da maza da mata a gidan ta.
“Ta na da son mutane. Ba ta da ƙyashi ko baƙin ciki.
“Ta daɗe da daina ‘producing’ ɗin fim, amma duk abin da ya zo na cigaban masana’antar za ka gan ta a ciki. Tabbas, an yi rashin uwa!
“Allah ya jiƙan ta, ya kyautata makwancin ta, ya ba wa iyalin ta da sauran abokan arziki haƙurin rashin ta.”
Mu ma a mujallar Fim mu na roƙon Allah ya yi mata rahama, ya albarkaci abin da ta bari, amin.
#fimmagazine

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button