Kannywood

Mun rabu lafiya da mahaifiyar mu – Aminu Alan Waka

SHAHARARREN sha’iri, Alhaji Aminuddeen Ladan Abubakar (Alan Waƙa) ya bayyana cewa sun rabu lafiya da mahaifiyar su, wadda Allah ya yi wa rasuwa a daren jiya Litinin kuma aka kai ta kushewa a safiyar yau.
Alan Waƙa ya faɗi haka ne a tattaunawar sa da mujallar Fim jim kaɗan bayan an binne mahaifiyar tasa, Hajiya Bilkisu Sharif Adam, a maƙabartar unguwar Tarauni.
Hajiya ta rasu a Kano sakamakon hawan jini wanda ta sha fama da shi tsawon shekara 40.
Ta rasu ta na da shekara 70 a duniya, kuma ta bar ‘ya’ya biyu – Aminu Ala da ‘yar’uwar sa Khadija Ladan Abubakar – da jikoki 25.
Dandazon al’ummar gari da su ka haɗa da manyan malamai, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ma’aikata, mawaƙa da jaruman fim sun halarci jana’izar.
Tun da farko, an gudanar da sallar jana’izar Hajiya Bilkisu a gidan Ala da ke unguwar Maidile da ƙarfe 9:06 na safe.
Daga nan ɗimbin jama’a su ka raka ta zuwa makwancin ta a maƙabartar Tarauni.

Aminu Ala a gaban kabarin mahaifiyar sa jim kaɗan bayan an rufe ta

Jim kaɗan bayan kammala binne gawar ne mujallar Fim ta ji ta bakin Alan Waƙa kan wannan babban rashi da aka yi, inda ya ce, “Ba abin da za mu bayyana sai dai mu ce bawa ya koma ga Ubangijin sa. Dukkan rai ya na jiran irin wannan rana.
“Mu na jaddada godiyar mu ga Allah da ya raba mu da iyayen mu lafiya, mahaifiya ta Hajiya Bilkisu Adamu da kuma Sharif Adamu Maidoki.
“Mun yi zaman amana, zaman lafiya da ita, kuma mun rabu lafiya, ta na yabo na, ta na yabon dukkanin sauran ‘ya’yan ta ma, kuma dukkanin dangin ta su na alfahari da ita.
“Marigayiya ma’abociyar zumunci ce, don ko shekaranjiya da jiya duka ta je zumunci, ta je dubiya asibiti, wanda hakan ne ya ƙara rikita jikin nata. Da man ta na fama da ciwon hawan jini sama da shekara arba’in, amma kuma mai kula da shan magani ce da kuma ƙa’ida, shi ya sa abin ya yi tsawaici, ba ya ba ta matsala.”
Kazalika, mawaƙin kuma marubuci ya bayyana godiyar sa ga waɗanda su ka halarci jana’izar. Ya ce, “Shakka babu, mutane sun nuna halacci, kuma hakan ya nuna ana zaune lafiya, musamman abokan sana’a da kuma iyaye.
Alan waka Yana Share Hawaye

 
“Ina jaddada godiya ga Mai Martaba Sarkin Kano da ya taso sakataren masarauta da ya halarci wannan jana’iza a madadin Sarki da muƙarraban sa gaba ɗaya, sannan kuma da ‘yan siyasa su ma sun zo.
“Wannan ya nuna tabbatuwar hulɗar arziki kenan da ake yi. Sannan ga abokan sana’a mawaƙa da marubuta na gan su da yawa. Sannan akwai ‘yan fim da su ke harkar finafinai, su ma na ga fuskokin su fitattu daga ciki wanda iya su ma sun wakilci sauran ‘yan fim ɗin.
“To ina jaddada godiya da wannan karamci da su ka nuna da kuma kara, wanda ya nuna da man ana tare, kuma shi rashi abin da ya shafi kowa ne.
“Mu na yi wa Allah godiya ƙwarai da gaske da dukkan al’ummar da su ka samu halarta. Akwai wasu da dama da ba su samu ikon zuwa ba, amma sun biyo mu da addu’a. Wasu su ma ba su da lafiya, wasu kuma uzuri ne, amma idan sun yi addu’ar duk daidai ne; kowa Allah ya na ba shi lada gwargwadon aikin sa da ya yi da kuma niyya, da ma waɗanda su ka taso daga sassan garuruwa da dama, duk na gode musu. Allah ya saka da alkairi.”
Kabarin Hajiya Bilkisu Sharif Adam jim kaɗan bayan kammala jana’iza

 
Daga cikin manyan mutanen da su ka halarci jana’izar akwai shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, da fitaccen shehin malamin nan na Jami’ar Bayero, Kano, Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, da ɗan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP a shekarar 2019, Alhaji Abba Kabir Yusuf (wato Abba Gida-Gida).
Wasu daga cikin jarumai da mawaƙa da mujallar Fim ta yi tozali da su a wurin wannan jana’iza sun haɗa da Ali Nuhu, Mustapha Nabraska, Ali Gumzak, Falalu A. Ɗorayi, Malam Bashir Ɗandago, Abba El-Mustapha, Sulaiman Farfesan Waƙa, Nazir Ɗanhajiya da ma wasu.
Mu ma a mujallar Fim mu na addu’ar Allah ya jiƙan Hajiya Bilkisu, ya ci gaba da kyautata zuri’ar ta, amin.
Aminu Ala da sauran jama’a su na yi wa Hajiya Bilkisu addu’a a gaban kabarin ta

 
Mun dauko duk wannan tattaunawar daga fim maganazineMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button