Kannywood

Matan Kannywood Muna Fama Da Rashin Ilimi Da Jahilci Yakamta mu Koma Makaranta ~Rukayya Dawayya

Matan Kannywood Muna Fama Da Rashin Ilimi Da Jahilci Yakamta mu Koma Makaranta ~Rukayya Dawayya
Matan Kannywood Muna Fama Da Rashin Ilimi Da Jahilci Yakamta mu Koma Makaranta ~Rukayya Dawayya
Hoto : Instagram
Daga : Rukayya Dawayya

Tsohuwar Jaruma kuma mai shirya fina finai a masanantar Kannywood Rukayya Umar Santa wacce aka fi sani da Rukayya Dawayya ta ce ya kamata Jarumai Mata na masanaantar Kannywood su koma Islamiyya.
Ta ce ta kula dukkan wasu matsaloli da rigingimu ko kuma daukar magana dake faruwa a Kannywood Jarumai Mata ne ke jawo su.
Ita mace Uwa ce kuma mai koyar da tarbiyya bare kuma su jaruman Kannywood tarbiyya aka san su da koyarwa ya kamata aga tarbiyya daga gare su; inji ta
Rukayya Dawayya, ta kara da cewar ta kula wasu abubuwan da Jahilci da rashin ilimi ake yin su saboda haka dukkan wacce tasan bata da ilimi daga cikin su har da ita ma ya kamata su koma islamiyya don su sami ilimin Addini.
Jarumar ta bayar da wannan shawarar ne a wani faifayin Bidiyo data wallaha a shafin ta kuma da alama tana yin martani ne game da hukuncin shariar da aka yankewa Jarumar Masanaantar su ta Kannywood Sadiya Haruna ne.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar Dawayya, ta ce tun tana yar ƙarama take zuwa islamiyya kuma har yanzu bata dena ba.
Akwai masu ilimi a cikin mu da yawan gaske amma jahilan cikin mu sun fi yawa.
Ga bidiyon nan kasa zaku iya saurara kuji daga bakinta.

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Rukayya Dawayya (@dawayyarukayya85)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button