Addini

Kungiyar Izala zata shuka bishiya miliyan 2 A Najeriya

Kungiyar Izala zata shuka bishiya miliyan 2 A Najeriya
Kungiyar Izala zata shuka bishiya miliyan 2 A Najeriya

Majiyarmu ta samu wannan labarin daga shafin dailynigerian hausa sunka wallafa Wanda suma nuna daga shafin wisal tv ne.
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa’ikamatus Sunnah Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewar kungiyar Izala ta shirya tsaf domin ganin shuka bishiyoyi kimanin guda miliyan biyu a fadin Najeriya.
Shugaba Bala Lau ya bayyana hakan ne yayin bikin kaddamar fara shuka bishiyun da aka gudanar a jihar Katsina ‘yan kwanakin da suka gabata.
Shugaban kungiyar Sheikh Bala Lau yace, Izala tayi nufin shuka bishiyun ne domin taimakawa kare muhalli da Ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa da ake samu a wasu saddan kasarnan.
Haka kuma, shugaban kungiyar ya bayyana cewar, shugabannin kungiyar na jihohin Najeriya ne zasu wakilci shugaban Izala na kasa wajen gudanar da dashen itatuwan a garuruwansu da kuma jihohinsu.
WISAL TV

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button