Addini

Kudin da maza ke kashewa Waya ya isa su Rike Aure – Dr Abdallahi G/Kaya

Advertisment

Kudin da maza ke kashewa Waya ya isa su rike aure – Dr Abdallahi G/Kaya
Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan da ke unguwar Gadon Kaya, Dr. Abdallah Usman Umar, ya ce, kashe kudaduen da wasu mazaje ke yi wajen siyan Data a wayoyinsu, ya fi dacewa su yi amfani da kudaden a yi aure.
Dala Fm Sun ruwaito.Dr. Abdallah Gadon Kaya, ya bayyana hakan ne, ta cikin shirin Rayuwa Abar Koyi na gidan redoyin Dala, wanda ya gudana a ranar Juma’a.
Ya ce, “Mafi yawan lokuta mazajen, kan amfani da tarin kudin su a wayoyi, ta hanyar siyan Datar, amma kuma su na fakewa da cewar ba su da kudin karin aure, a bangare guda kuma ‘yan mata da zaurawa sun yi yawa babu aure”.
Ya kuma ce, “Maimakon sabbin Babura da wayoyi da su ke siya, ya fi dacewa su rinka amfani da kudaden, ta hanyar yin aure, domin kaucewa fadawa cikin wani hali”. Inji Dr. Abdullahi.
Wakilin mu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, Dr. Abdallah Usman Umar, ya kuma shawarci mata da su saukaka lamuran aure, domin a wasu lokutan tsauwalawar da wa su ke yi kan bawa mazajen tsoron tinkarar auren.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button