Labarai

Kalli Hotunan Yar Shekara 35 Ta Yi Wuff Da Yaro Dan Shekara 18

Wata mata mai suna Aisha Abubakar ‘yar shekara 35 zata aure saurayin dan shekara 18.

Amarya Aisha Abubakar Da Angonta Gaddafi Isah

Matar mai suna Aisha Abubakar ta kasance ‘yar asalin garin Tambuwal ce dake jihar Sokoto.

Shi kuwa saurayin mai suna Gaddafi Isah dan asalin garin Argungun ne dake jihar Kebbi.
A zantawarta da Jaridar Mikiya, amarya Aisha Abubakar ta ce zata auri saurayin nata ne saboda ta raya sunnar Annabi Muhammad (s.a.w), shi yasa batayi la’akari da shekarun yaron da zata aura ba. Ta kara da cewa shi aure ibada ne, haka kuma ba laifi bane mace ta auri wanda ta girma ba.

Amarya Aisha Abubakar Da Angonta Gaddafi Isah

Amaryar ta kara da cewa ita a wajenta angonta ba Yaro bane, tunda shi namiji shine yake gaba da mace a zamantakewar aure da rayuwar Duniya.
Za a daura auren Aisha Abubakar da angonta Gaddafi Isah Ranar Asabar mai zuwa, a garin Tambuwal dake jihar Sokoto.

Daga karshe amarya Aisha Abubakar ta nemi jama’a da su tayasu da addu’ar neman zaman Lafiya.

Amarya Aisha Abubakar Da Angonta Gaddafi Isah

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button